An Garkame Fursunoni 300 a Gidan Yarin Kano Ba Tare da Aikata Laifin Komai Ba, ’Yan Sanda

An Garkame Fursunoni 300 a Gidan Yarin Kano Ba Tare da Aikata Laifin Komai Ba, ’Yan Sanda

  • Yayin da wasu ke zaune a gidan gyaran hali kan laifuffukan da suka aikata, wasu kuma na zaman yarin ne ba tare da laifin komai ba
  • Wani fursuna mai suna Ibrahim Dala, ya ce ana tuhumarsa da laifin kisan kai amma tun bayan da aka tsare shi a shekarar 2009 ba a kai shi kotu ba
  • Wannan na daga cikin laifukan take hakkin dan Adam da 'kwamitin lauyoyi mashawarta' na rundunar 'yan sanda ya gano a gidan yarin jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Rundunar 'yan sanda ta gano wasu fursunoni sama da 300 da ke zaman gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano, ba tare da wata takarda ta bayanin shari’arsu ba.

Kara karanta wannan

Bayan Dangote, jama'a sun tare motar BUA, an wawushe kayan abinci ana tsakiyar yunwa

Rundunar ta gano hakan ne bayan da Sufeta Janar na rundunar, Kayode Egbetokun, ya kafa wani 'kwamitin lauyoyi mashawarta' don gudanar da irin wannan binciken.

Gidan gyaran hali. Kano
Yan sanda sun bankado laifukan tauye hakkin dan Adam a gidan yari na Kano.
Asali: UGC

Aikin da kwamitin ke yi a gidan yari

Kwamitin ya gano hakan ne a ranar Laraba a ci gaba da ziyarar da ya ke kai wa gidajen gyaran hali da kuma gidajen ladabtar da kananan yara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad-Hussaini Gumel ne ke jagorantar kwamitin.

Aikin kwamitin shi ne gudanar da bincike domin gano laifukan take hakki na mutanen da ke fuskantar shari'ar manya da kananun laifuka.

Fursunoni na zaman yari ba tare da hukunci ba

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ziyarar, Gumel ya ce aikinsu shi ne gano irin wadannan laifuka, rubuta su da kuma mika su ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

Da yake gabatar da wasu fursunonin da ke jiran shari’a na tsawon shekaru a Kurmawa, wani jami’in gidan yarin, ya ce mafi yawansu an kawo su ne ba tare da shaidar kama su da laifi ba.

Ya kara da cewa wasu daga cikin fursunonin sun shafe shekaru a tsare ba tare da takamaiman kotunan da aka gurfanar da su ba, kuma ba su da bayanan shari’a.

Abin da wasu fursunoni ke cewa kan shari'arsu

Wasu kuma, a cewar Premium Times, an bar su a gidan yarin ne kawai saboda ba za su iya daukar nauyin lauya don kare su a kotu ba.

Wani fursuna mai suna Ibrahim Dala ya ce ana tuhumarsa da laifin kisan kai amma tun bayan da aka tsare shi a shekara ta 2009 ba a kai shi kotu ba.

Yahya Usman, wani fursuna ya ce a shekarar 2017 ne karo na karshe da aka kai shi kotu, yanzu kuma yana zaman wakafin ne ba tare da sanin makomarsa ba.

Kara karanta wannan

Yan wasan ƙwallon ƙafa 5 da aka dakatar da su saboda sun yi amfani da ƙwayar ƙarin kuzari

Sai dai Gumel ya ba da tabbacin cewa fursunonin da abin ya shafa za su samu adalci nan ba da jimawa ba.

Kano: An kama mutane uku da laifin ta da tarzoma

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Kano, ta ce ta kama mutane uku da ake zargi da laifin tayar da zaune tsaye a yayin da 'yan kasuwar magani ke kwashe kayansu.

Legit Hausa ta ruwaito cewa mutanen sun yi kokarin balla shaguna don satar kaya, bayan da kotu ta umarci 'yan kasuwar su tashi su koma sabuwar kasuwar 'Kano Economic City.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel