Wigwe: Hadimin Marigayi Ya Fadi Yadda Ya Kaucewa Tsautsayin Mutuwa Tare da Mai Gidansa
- Yayin da ake ci gaba da zaman makokin Herbert Wigwe, hadiminsa ya bayyana abin da ya faru kafin rabuwarsu
- Sola Faleye ya ce tun farko sun yi niyyar shiga jirgin tare amma ya sauya tunani saboda daukar kayansu
- Sola ya ce ya dauki kayansu a mota domin tabbatar da sun isa lafiya saboda jirgin ba zai iya daukar duka kayan ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hadimin marigayi tsohon shugaban bankin Access ya bayyana yadda ya sha da kyar bayan rashin tafiya tare da mai gidansa.
Sola Faleye ya ce hakan ya faru ne yayin da ya yanke shawarar daukar kayayyakinsu wanda ya hana shi tafiya da mai gidansa, Herbert Wigwe.
Menene Sola yake cewa kan Wigwe?
Faleye ya bayyana haka a wani faifan bidiyo yayin bikin ta'aziyyar marigayin wanda manyan mutane da dama suka halarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce da farko sun yi niyyar tafiya a jirgin amma daga bisani ya yi tunanin daukar kayansu a mota saboda jirgin ba zai dauki kayan ba.
Ya kara da cewa marigayi Wigwe da kansa ya yabawa tunaninsa domin ganin kayan sun isa lafiya ba tare da matsala ba.
Yadda Sola ya rabu da Wigwe
Sola ya dauki kayan ya nufi Vegas a mota yayin da Wigwe da matarsa da kuma ɗansa suka shiga jirgin mai saukar ungulu.
Faleye yayin da ya ke kan hanya ya kira lambar Wigwe amma baya shiga inda ya yi kokarin kiran sauran da suke tare duk da bai yi nasara ba.
Idan ba manta ba Wigwe ya mutu ne bayan hatsarin jirgi mai saukar ungulu wanda ya rusa da ɗansa da matarsa da kuma abokin kasuwancinsa.
Sunusi ya zubar da hawaye a zaman makokin Wigwe
Kun ji cewa tsohon sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi ya zubar da hawaye yayin zaman makokin marigayi Herbert Wigwe.
Sunusi ya bayyana yadda Wigwe ya taimake sa da iyalinsa lokacin da aka tumbuke shi a matsayin sarkin Kano.
Wannan na zuwa ne bayan Wigwe ya mutu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu wanda ya rusa da ɗansa da matarsa.
Asali: Legit.ng