Innalillahi: Bayan Kisan Gilla da Aka Yi Wa Malami, an Cafke 'Yan Bangan da Ake Zargi
- A jiya Talata ce 5 ga watan Maris aka yi wa wani malamin addini kisan gilla mai suna Abubakar Hassan Mada
- Ana zargin wasu 'yan sa kai da ke hukumar CPG da kisan malamin a garin Mada da ke Gusau a jihar Zamfara
- Sai dai a cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce wadanda aka kaman ba su da alaka da hukumar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cafke mutane 10 da ake zargin da kisan babban malamin addinin Musulunci.
Idan ba a mantaba an yi wa malamin, Sheikh Abubakar Hassan Mada kisan gilla a jiya Talata 5 ga watan Maris a garin Mada da ke birnin Gusau.
Su waye ake zargi da kisan malamin?
Ana zargin wasu jam'ian hukumar CPG da kisan malamin wadanda aka kirkire su domin kare al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai gwamnatin jihar ta musanta cewa akwai sa hannun hukumar a cikin kisan gillar, cewar Tribune.
Gwamnatin ta ce wadanda aka kaman 'yan sa kai ba su da alaka da hukumar da suka kirkira domin dakile matsalar tsaro.
Sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamna jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar.
Martanin Gwamnatin jihar
A cewar sanarwar, gwamnatin Zamfara ba ta lamunce wa ’yan bangan da aka kama gudanar da kowane irin aikin tsaro ba, saboda ba sa cikin rundunar kare jama'a ta jihar.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu labarin kisan gilla da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada. Lallai wannan abin takaici ne da za a iya kauce ma shi.
“Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke duk ’yan banga da ake zargi da aikata wannan ɗanyen aikin.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauki wannan lamari da muhimmanci kuma ta himmatu wajen ganin an gurfanar da duk waɗanda suka aikata wannan kisan gilla a gaban kotu."
- Sulaiman Bala
"Za a yi duk mai yuwuwa domin ganin an yi adalci ba tare da tsangwama ba, muna son fayyace cewa 'yan bangan da ake zargi da aikata kisan gilla ba su da wata alaƙa da Askarawan Zamfara."
- Sulaiman Bala
An kama shugaban Miyetti Allah
Kun ji cewa an kama shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Adamawa, Alhaji Jaoji Isa kan wasu zarge.
Ana zargin shugaban kungiyar, Isa da tatsar kudade har naira miliyan 2.4 ba bisa ka'ida ba inda rundunar ta fara bincike.
Asali: Legit.ng