Sheikh Bn Uthman Ya Fadi Alkawuran da Abba Yayi Masu Yayin Zama da Malaman Kano

Sheikh Bn Uthman Ya Fadi Alkawuran da Abba Yayi Masu Yayin Zama da Malaman Kano

  • Sheikh Muhammad Bn Uthman ya yi magana kan ganawar malaman addini da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a makon jiya
  • Shehin malamin ya ce maganar da Gwamna Abba Kabir ya yi a yayin zaman ya faranta masa rai matukar gaske kan wasu gyararraki
  • Malamin ya samu wakilcin daya daga cikin na’ibinsa da ya kira da Mala inda ya ce maza-maza ya je ya wakilce shi a zaman da aka yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Bn Uthman ya bayyana abin da Gwamna Abba Kabir ya fada musu.

Bn Uthman ya ce ya ji dadin abin da gwamnan ya fada masu wanda ya faranta masa rai sosai yayin zaman da suka yi da shi.

Kara karanta wannan

PDP ta samu baki yayin da gwamnanta a Arewa ya dira kan Buhari, ya fadi illar da ya yi wa Najeriya

Malamin addini ya fadi abin farin ciki da Gwamna Abba Kabir ya fada musu
Bn Uthman ya yabawa Abba Kabir kan alkawarin da ya yi musu. Hoto: @Kyusufabba, @Bnuthmanm.
Asali: Twitter

Kano: Menene Bn Uthman ya ke cewa kan Abba Kabir?

Malamin ya ce gwamnan ya yi alkawarin gyaran masallatan Juma’a na Kano da kuma agazawa limamai a fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin malamin ya ce Gwamna Abba Kabir ya kuma roki malaman da su kira su, su yi musu gyara a duk lokacin da suka kauce hanya.

“Alhamdulillah zaman da aka yi da mai girma gwamnan Kano da malamai abin ya faranta mani rai gaskiyar magana.
“Cikin bayanan mai girma gwamna ya ce za su gyara masallatan Juma’a wannan abin da faranta rai da kuma agazawa limamai muhimmin lamari ne."

- Muhammad Bn Uthman

Sulhu tsakanin Abba Kabir da Hisbah Kano

Wannan na zuwa ne bayan sulhu da aka yi tsakanin Gwamna Abba Kabir da kuma hukumar Hisbah a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sasanta da Aminu Daurawa, ya koma kwamandan Hisbah gadan-gadan

Sulhun ya biyo bayan murabus din shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga kujerarsa kan wasu maganganun Gwamna Abba Kabir.

Murabus din Daurawa ya jawo cece-kuce sosai da zazzafar muhawara kan abin da ya jawo matsalar da ta saka Daurawa murabus.

Kwankwaso ya yi magana kan Daurawa

Kun ji cewa, jigon APC a jihar Kano, Ilyasu Musa Kwankwaso ya yi magana kan murabus din Sheikh Daurawa da ya yi daga mukaminsa.

Musa Kwankwaso ya ce daman ya fada hakan za ta faru kuma yanzu ga shi abin da suke tsoron ya afku a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel