Dangote, Otedola da Minista Za Su Bunkasa Makarantun Koyon Aikin Shari'a Na Najeriya

Dangote, Otedola da Minista Za Su Bunkasa Makarantun Koyon Aikin Shari'a Na Najeriya

  • Makarantar koyon aikin shari'a ta Najeriya za ta samu muhimman ayyuka daga wajen Aliko Dangote da Femi Otedola
  • Femi Otedola zai gina gidajen ma'aikata a harabar makarantar da ke Legas yayin da Dangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai a harabar makarantar da ke Kano
  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, zai samar da gidajen ma'aikata a harabar makarantar da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Femi Otedola, Aliko Dangote, da Nyesom Wike za su gina ƙarin gidajen ma'aikata da ɗakunan kwanan ɗalibai a makarantun koyon aikin shari'a na Najeriya.

Jaridar Nairametrics ta ce darakta janar na makarantar, Farfesa Isa Hayatu, shi ne ya tabbatar da hakan inda ya yaba musu kan wannan kyakkyawar niyyar ta su.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hotuna sun bayyana yayin da aka gudanar da salloli na musamman a Zaria

Femi Otedola da Dangote
Dangote, Otedola za su gina gidajen ma'aikata da dakunan kwanan dalibai Hoto: Femi Otedola, Dangote Group
Asali: UGC

Makarantar koyon aikin shari'a ta Najeriya, wacce ta yi fice sama da shekaru 60, ita ce ginshiƙin ilimin shari'a a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗannan ayyukan da za a gudanar sun nuna yadda ake samun ƙaruwar buƙatar ilmin shari'a a Najeriya, da rawar da makarantun suke takawa a ɓangaren shari'a.

A ina Dangote, Otedola, Wike za su yi ayyukan?

Hamshaƙin attajirin nan Femi Otedola zai gina gidajen ma'aikata a harabar makarantar da ke Legas, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Aliko Dangote ya yi alkawarin gina sabbin ɗakunan kwanan ɗalibai a harabar makarantar da ke Kano.

A nasa ɓangaren, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, Abuja, zai gina gidajen ma’aikata a harabar makarantar da ke Abuja tare da samar da motocin aiki.

Waɗannan ayyukan sun zo a daidai lokacin da ake buƙatarsu, yayin da makarantar fuskantar ƙalubalen samar da wuraren kwana ga ɗaliban da ke neman samun gurbi a cikinta.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya yun yi luguden wuta kan ƴan ta'adda, sun tura da dama lahira

Alƙawuran na Otedola, Dangote da Wike ga makarantun zai ƙara bunƙasa wuraren koyon karatun ɗaliban.

Waɗannan ayyukan idan aka kammala su za su ƙara ɗaga darajar karatun shari'a a Najeriya.

Arziƙin Dangote Ya Yi Sama

A wani labarin kuma, kun ji cewa arziƙin hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ƙaru.

Wannan ƙarin dukiyar da attajirin ya samu ya sanya ya dawo matsayin mutum na 132 a cikin jerin attajiran da suka fi kowa kuɗi a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel