Ana Kukan Ba Kudi, Wike Zai Gina Katafariyar Makarantar Sakandare a Abuja, Za Ta Lakume N1.7bn

Ana Kukan Ba Kudi, Wike Zai Gina Katafariyar Makarantar Sakandare a Abuja, Za Ta Lakume N1.7bn

  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta gina wata makarantar sakandare ta zamani a Abuja, wacce za a kashe naira biliyan 1.7 wajen gina ta
  • Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ya ce za a kammala gina makarantar a cikin shekara daya
  • Wike ya kuma tabbatar da cewa makarantar za ta yi gogayya da makarantun duniya wajen ba dalibai ilimi ta hanyar amfani da fasahar zamani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja (FCTA) za ta kashe Naira biliyan 1.7 daga kasafin 2024 don gina makarantar sakandare ta zamani a FCT.

Ministan FCT, Nyesom Wike ya sanar da hakan a Abuja a ranar Alhamis, a wani taro da aka shirya na nuna kokarin daliban makarantun gwamnati na Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu ta fara yanke hukunci kan shari'ar BBC da wani mawakin Kano

Wike zai kashe naira biliyan 1.7 don gina makarantar sakandare a Abuja
Wike zai kashe naira biliyan 1.7 don gina makarantar sakandare a Abuja. Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Wike, wanda ya samu wakilcin wani sakatare a sakatariyar ilimi ta FCTA, Dr Danlami Hayyo, ya ce gina makarantar zai bunkasa ilimin fasahar zamani da na yanar gizo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naira biliyan 1.7 na daga cikin kudin gyaran makarantu a 2024

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ya ruwaito Dr Hayyo na cewa za a gina makarantar a garin Karshi da ke karkashin karamar hukumar Abuja cikin gari, kuma za a zuba mata kayan aiki.

Ya bayyana cewa naira biliyan 1.7 da za a gina makarantar na daga cikin naira biliyan 13.1 da aka ware don gyaran makarantu a kasafin FCT na 2024.

Ministan ya ce bayan kammala gina makarantar, za kuma a samar da kayayyakin koyarwa na zamani a sauran makarantu don inganta ilimin fasahar zamani ga dalibai.

Makarantar za ta yi gogayya da makarantun duniya na zamani

Kara karanta wannan

Betta: Gbajabiamila ya amince da N2bn ba tare da izinin Tinubu ba? Fadar shugaban kasa ta yi martani

Wike wanda ya nuna yakinin za a iya kammala ginin makarantar a cikin shekara daya, ya ce za a saka na'urorin zamani, fasahar amfani da yanar gizo da sauran su.

Makarantar a cewar Wike, za ta kasance ta kwana ce ga dalibai, kuma za a saka dukkan kayayyakin koyon karatu ta yanar gizo don saukaka koyarwa, rahoton Daily Nigerian.

Gwamnan Kano ya fara rabon kayan abinci ga ma'aikatan jihar

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara rabon kayan abinci ga ma'aikatan kananan hukumomi a jihar don rage radadin janye tallafin man fetur.

Ma'aikatan da za su fara samun wannan tallafi su ne masu matakin albashi daga GL 01 zuwa 06, inda aka ba su shinkafa da masara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel