Dangote zai gina hanyar Birnin Gwari domin Gwamnati tayi masa afuwar haraji - El-Rufai

Dangote zai gina hanyar Birnin Gwari domin Gwamnati tayi masa afuwar haraji - El-Rufai

Mai girma gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta nemi babban Attajirin nan watau Alhaji Aliko Dangote ya gina wani babban titi a cikin jihar.

Dangote zai gina hanyar Birnin Gwari domin Gwamnati tayi masa afuwar haraji - El-Rufai
Kamfanin Dangote zai gina hanyar Garin Birnin Gwari
Asali: UGC

Malam Nasir El-Rufai yace Alhaji Aliko Dangote zai gina titin Kaduna zuwa Birnin Gwari har zuwa cikin jihar Neja. Gwamnan yace an ba ‘dan kasuwar wannan aiki ne a matsayin sharadin yi masa rangwamen harajin da ke kan sa.

Hamshakin Attajirin ya bayyanawa mutanen birnin Gwari wannan ne a lokacin da ya kai ziyara zuwa yankin inda ya tattauna da mutanen Garin. Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa za a kawo karshen rikicin da ake yi a yankin.

KU KARANTA: Aljihun ‘Dan takarar 2019 yayi kuka baya ya kashe sama da N200m a kamfe

Yanzu haka gwamnatin tarayyar Najeriya za ta ba kamfanin Dangote wanda shi ne mai kudin Afriklamunin harajin da ke kan sa da nufin cewa zai gyara titin Birnin Gwari wanda ke tsakanin jihar Kaduna da kuma jihar Neja.

Gwamnan na Kaduna yayi amfani da wannan dama ya kuma bayyana irin kokarin da gwamnatin APC ta ke yi wajen kawo karshen matsalolin jihar musamman a game da sha’anin tsaro. A karshe kuma ya gabatar da ‘yan takarar sa.

A makon nan ne mu ka ji cewa dukiyar Attajirin yayi kasa a shekarar bara inda mujallar Frobes tace abin da Dangote ya mallaka ya gangaro kasa daga Dala biliyan 12.5 zuwa kusan Dala biliyan 10.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel