Majalisar Wakilai Ta Dauki Mataki Bayan Gano Abin da Ya Jawo Karancin Abinci a Najeriya
- Majalisar wakilai ta ce matsalar tsaro da ta dade tana addabar Najeriya musamman yankin Arewa ya jawo karancin abinci a kasar
- Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu ya bayyana haka a taron muhawarar da aka yi a zauren majalisar a ranar Talata
- Ministan noma, Abubakar Kyari shi ma ya yi bayani kan dalilan da suka jawo tsadar rayuwa a kasar da matakin da gwamnati ta dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Majalisar wakilai ta ce rashin tsaro da aka dade ana fama da shi a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya ya jawo karancin samar da abinci a kasar.
Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu ya bayyana haka a jawabin bude taron muhawarar da aka yi a zauren majalisar a ranar Talata.
Matsalar abinci a Najeriya
Ya ce karancin abinci ya shafi al’amuran zamantakewa da tattalin arziki a kasar kuma yana yin barazana ga zaman lafiyar al'ummar kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ruwaito ministan noma, Abubakar Kyari, ya ce tilas ne Najeriya ta zuba jari sosai a harkar noma don farfado da tattalin arziki maimakon ayi noma don cin abinci kawai.
Gwamnati na shiri domin taimakawa manoma - Kyari
Ya lura cewa kananan manoma ne ke noma mafi rinjayen abincin da Najeriya ke amfani da shi, alhalin ba su da wadatar arzikin noma mai yawa sai don su rayu a kansa.
Kyari ya kara da cewa akwai shirye-shirye da dama da gwamnati ta yi da suka shafi dubban manoma a kasar domin inganta noman shinkafa, alkama, rogo da sauran su.
Jaridar Vanguard ta ruwaito ministan ya ce gwamnati ta fara tattaunawa da manya-manyan kungiyoyin noma kamar WACOT, Olam da sauran su kan aikin noma mai inganci.
Gwamnati za ta samar da taraktoci da taki - Kyari
Ya koka da cewa Najeriya na da bukatar taraktar noma 70,000,amma a halin yanzu guda 5,000 ne kadai ke aiki a kasar.
Sai dai ya ce gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wani kamfani na Amurka domin kawo taraktoci 10,000 cikin shekaru biyar.
Ministan ya kuma ce gwamnati ta fara tattaunawa da manyan kamfanonin sarrafa taki na zamani domin magance matsalar farashi da wadatuwarsa ga manoma.
Gwamnati za ta kawo karshen tsadar abinci - Kyari
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya ce gwamnati ta dauki matakai don kawo karshen tsadar rayuwa a Najeriya.
Kyari ya fara dora alhakin bakar wahalar da ake sha a Najeriya kan fitar da abinci da ake yi zuwa kasashen waje ba bisa ka'ida ba, da kuma ambaliyar ruwa a kasar.
Ya ce shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba ma'aikatar noma umarnin daukar duk wani mataki da zai kawo sauki ga rayuwar 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng