Hikima! Wani yaro ya kera babur daga karafan bola a Arewacin Najeriya

Hikima! Wani yaro ya kera babur daga karafan bola a Arewacin Najeriya

Wani yaro da ya fito daga jihar Benue dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya mai suna Oloche yayi abun azo a gani bayan da ya bar jama'a cikin al'ajabi lokacin da ya hada babur da wasu abubuwan hawa na zamani da karafan da yake tsintowa a bola.

Shi dai wannan yaro mai suna Oloche mun samu cewa ya fito ne daga kauyen Otada dake a jihar ta Benue kuma yanzu haka yana karatu ne a makarantar Sakandare.

Hikima! Wani yaro ya kera babur daga karafan bola a Arewacin Najeriya
Hikima! Wani yaro ya kera babur daga karafan bola a Arewacin Najeriya

Legit.ng dai ta samu cewa wani ma'abocin anfani da kafar sadarwa ne ta Adikwu Josh ya fara yada hotunan yaron mai fasaha kafin daga baya lamarin ya ba jama'a da dama sha'awa.

A wani labarin kuma, Yanzu haka labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa akalla jam'iyyu sha tara ne ke shirin dunkulewa wajen guda domin kalubalantar manyan jam'iyyun da ke garemu yanzu a Najeriya na APC da kuma PDP.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga jagoran shirin dunkulewar kuma shugaban daya daga cikin jam'iyyun watau Freedom and Justice Party (FJP), mai suna Dakta Onwubuya Breakforth inda yace tuni shire-shire sun yi nisa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng