Babbar Magana: An Tsaurara Matakan Tsaro a Zauren Majalisar Dokokin Jihar Arewa Kan Matsala 1

Babbar Magana: An Tsaurara Matakan Tsaro a Zauren Majalisar Dokokin Jihar Arewa Kan Matsala 1

  • Dakarun ƴan sanda sun mamaye majalisar dokokin jihar Filato yayin da korarrun ƴan majalisar PDP ke shirin haddasa matsala
  • Wata majiya daga cikin jami'an tsaron ta ce an ba su umarnin bincikar duk wanda zai shiga majalisar domin daƙile masu shirin tayar da yamutsi
  • Mambobin majalisar jihar Filato 16 waɗanda kotun ɗaukaka ƙara ta tsige sun lashi takobin ci gaba da halartar zaman majalisa a yau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta girke ƙarin dakarun ƴan sanda a zauren majalisar dokokin jihar yayin da rikicin siyasa ya ɗauki sabon salo.

Wannan matakin na zuwa ne yayin da ƴan majalisar dokoki 16 na jam'iyyar PDP suka sha alwashin komawa zauren majalisar duk da kotun ɗaukaka ƙara ta kore su.

Kara karanta wannan

An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa

Yan sanda sun tsaurara tsaro a majalisar dokokin Filato.
Jami'an Yan Sanda Sun Tsaurara Tsaro a Zauren Majalisar Dokokin Jihar Filato Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Rahotan Leadership ya nuna cewa an tura ‘yan sanda dauke da makamai zuwa wurin zaman mambobin majalisar a tsohon gidan gwamnati tunda misalin karfe 5 na asubahi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jami'in ɗan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an ba su umarnin bincikar duk wanda zai shiga wurin domin banbance ma'aikata da maus shirin tada yamutsi.

Meyasa ƴan sanda suka ɗauki wannan matakin?

An ƙara jibge tulin jami'an ƴan sanda a majalisar ne domin daƙile duk wani yunƙuri na tada zaune tsaye ko mamaye zauren da miyagu ka iya zuwa su yi a zaman yau Talata.

Rahoton Daily Trust ya ce ana fargabar yiwuwar samun rikici tsakanin ‘yan majalisar PDP 16 da kotun daukaka kara ta kore su da kuma ‘yan majalisar APC da kotun ta bai wa nasara.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Har kawo yanzu dai babu ko ɗaya daga cikin mambobin majalisar na APC ko na PDP da suka isa zauren majalisar na wucin gadi da ke harabar tsohon gidan gwamnati.

Kakakin majalisa ya yi magana kan nasarar Gwamna Sule

A wani rahoton kuma Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa ya aike da saƙo ga yan adawa bayan karkare shari'ar zaben Nasarawa a kotun ƙoli.

Honorabul Ɗanladi Jatau ya buƙaci yan adawa su haɗa hannu da gwamnatin Abdullahi Sule domin kyautata rayuwar al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel