NLC: Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Abu 1 da Zai Hana Ta Shiga Yajin Aiki
- Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta rubutawa gwamnatin tarayyar Najeriya wasiƙa a yunƙurinta na ganin Najeriya ta zama ƙasa mai kyau
- A cikin wasiƙar, NLC ta yi watsi da iƙirarin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta cika kaso 80% na yarjejeniyar ranar 2 ga watan Oktoban 2023 da suka cimmawa
- Ƙungiyar ta NLC ta haƙiƙance cewa yawancin yarjejeniyoyin da aka cimmawa har yanzu gwamnati ba ta cika su ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta haƙiƙance cewa aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimmawa ne kawai zai dakatar da yajin aikin gama gari da take shirin yi a faɗin ƙasar nan.
A cikin sabuwar wasiƙar da ta rubuta zuwa ga ƙaramar ministan kwadago da samar da ayyuka, ƙungiyar NLC, ta buƙaci gwamnatin Bola Tinubu da ta aiwatar da alƙawurran da ta ɗauka wa ma’aikata da ƴan Najeriya.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito a ranar Litinin, 4 ga watan Maris, NLC ta shawarci gwamnati da daga yanzu zuwa ranar 13 ga watan Maris, 2024, ta gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin don kaucewa shiga yajin aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me NLC ta ce a cikin wasiƙar?
Jaridar Guardian ta kawo rahoto kan wasiƙar da NLC ta aikewa gwamnatin jam'iyya mai mulki watau APC.
Wani ɓangaren na wasiƙar yana cewa:
"Bayan an yi nazari da kyau na batutwa 15 da aka zayyana a cikin yarjejeniyar 2 ga watan Oktoban 2023, a bayyane yake cewa yawancinsu ba a cika su ba.
"Bugu da ƙari kuma, ƴan kaɗan ɗin da aka aiwatar, ba a aiwatar da su yadda ya dace ba."
- NLC
'Yan NLC sun yi zanga-zanga
A watan Fabrairu ne ƙungiyar NLC ta gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyoyin da ta ƙulla da ƙungiyar.
An dai ƙulla yarjejeniyar ne biyo bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023 wanda ya haifar da karin farashin kayayyaki a faɗin ƙasar nan.
Daga bisani, NLC ta dakatar da zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar nan, inda ta bayar da wa'adin ranar 13 ga watan Maris ga gwamnatin tarayya.
An Caccaki Ƙungiyar Ƙwadago
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani tsohon jigo a jam'iyyar PDP ya caccaki ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), kan dakatar da zanga-zanga
Deji Adeyanju ya yi nuni da cewa ƙungiyar ta zubar da ƙimar da take da ita a idon ƴan Najeriya saboda dakatar da zanga-zangar.
Asali: Legit.ng