Ana Cikin Halin Kunci, Tinubu Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga 'Yan Najeriya

Ana Cikin Halin Kunci, Tinubu Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga 'Yan Najeriya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ganin an gyara Najeriya ta koma kan turbar da ta dace
  • Tinubu ya jaddada ƙudirinsa na ganin ya jagoranci Najeriya wajen samun ci gaban tattalin arziƙi da zamantakewa
  • Shugaba Tinubu ya dage cewa sauƙi na nan tafe nan bada jimawa ba, kuma ya ɗauki alhakin halin da ake ciki yanzu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Shugaban ƙasa Bola Tinubu, a ranar Laraba, ya roki ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki, inda ya ba da tabbacin cewa sauƙi na nan tafe.

Shugaban ya ce yana da cikakkiyar masaniya kuma ya ɗauki alhakin matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya keɓe minista 1, ya yaba masa kan yadda ya share hawayen ƴan Najeriya

Tinubu ya ba 'yan Najeriya hakuri
Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce ba zai yi ƙorafi ba amma yana maraba da duk sukar da ake yi masa tunda shi ne ya nemi zama shugaban Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ziyarar da ya kai wa shugaban ƙungiyar ƴan ƙabilar Yarabawa ta Afenifere.

Legit Hausa ta ruwaito cewa, shugaban ya je jihar Ondo ne musamman domin ta'aziyya ga iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.

Wane tabbaci Tinubu ya ba ƴan Najeriya?

Tinubu ya ce:

"Najeriya za ta tsira daga ƙalubalen tattalin arziƙi da ake fuskanta. Akwai alamomin nasara. Ni na nemi aikin kuma ba na yin gunaguni game da shi. Na ɗauki alhaki kan komai."

Bugu da ƙari, Tinubu ya ce ya yaba da fahimtar da ƴan Najeriya suka yi masa a wannan mawuyacin lokaci amma ya tabbatar musu da cewa haƙurinsu da jajircewarsu ba za su tafi a banza ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tsohon gwamna ya nemo mafita ga 'yan Najeriya

A kalamansa:

"Ƙalubalen tattalin arziki da muka shiga tun lokacin da na hau mulki ba sabon abu bane a gare ni. A matsayina na tsohon gwamnan jihar Legas, na fuskanci irin wannan kiraye-kirayen na yin murabus.
"Amma, ta hanyar jajircewa, Legas ta zama ta biyar mafi ƙarfin tattalin arziki a duk nahiyar Afirika. Dole ne mu tafiyar da wannan lokacin da hikima kuma mu bunƙasa Najeriya cikin gaskiya.
"Na nemi wannan ofishin domin biyan buƙatun Najeriya, kuma aka zaɓe ni. Wasu sun ce ba zan kai labari a kotun zaɓe ba kuma sun yi hasashe iri-iri, amma ko a kotu, na ci gaba da mayar da hankali.

Shugaba Tinubi Ya Yabawa Ministansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban lasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yabawa Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida, kan sauye-sauye masu amfani da ya ɓullo da su a ƙasar nan.

Shugaban ƙasan ya yi nuni da cewa sauye-sauyen da ministan ya kawo sun rage koke-koken da ƴan Najeriya suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel