An Nemi Najeriya an Rasa da IMF Ta Saki Sunayen Kasashe 10 Mafi Arziki a Afirka a 2024

An Nemi Najeriya an Rasa da IMF Ta Saki Sunayen Kasashe 10 Mafi Arziki a Afirka a 2024

  • Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya fitar da jerin kasashe a Afirka da ke da mafi girman tattalin arziki (GDP) bayan shiga shekarar 2024
  • A cikin jerin, ba a ga sunan Najeriya ba, kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, bayan da IMF ya saka sunan Libya, Mauritius, da sauransu
  • Wannan sabuwar kididdigar ta shafi adadin kayayyaki da ayyukan da kowace kasa ta iya samarwa a wani kayyadadden lokaci da aka diba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ma'aunin jimillar karfin tattalin arzikin kasa (GDP) yana taka muhimmiyar rawa wajen tantance kasashe mafi arziki a Afirka, wanda ke auna kimar dukkan kayayyaki da ayyukan da ake samarwa kowane dan kasa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta shiga jerin kasashen da suka fi dadin zama a duniya, ita ce ta 8 a Afrika

Kididdigar kwanan nan na kasashe mafi arziki a Afirka yana dauke da kananan kasashe kamar Mauritius da Libya, bisa la’akari da daidaiton sayayyar kayayyakinsu (PPP).

Shugaba Al Sis na Masar, Mokgweetsi Masisi na Botswana da Prithvirajsing Roopun na Mauritius.
Karshen ƙarshen a jerin su ne Afirka ta Kudu, Algeria, Tunisiya, da Morocco. Hoto: PETER KLAUNZER / Contributor
Asali: Getty Images

Yadda ma'aunin GDP ke da tasiri a kididdigar

Ana kuma fitar da kididdigar ne ta hanyar lissafin hauhawar farashi da bambance-bambancen farashin kayayyaki, da kuma ba da ingantaccen kiyasi na mizanin tattalin arzikin jama'ar waɗannan ƙasashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahotan Business day asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya fitar da jerin kasashe 10 mafi arziki a Afirka ta hanyar ma'aunin jimillar karfin tattalin arzikin kasa na watan Fabrairun 2024.

Jerin kasashe 10 mafi arziki a Afirka a 2024:

Mauritius

Mauritius ce ke kan gaba a jerin IMF a matsayin kasa mafi wadatar arziki a Afirka a 2024, tare da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na dala 31,157.

Kara karanta wannan

'Yan kabilar Igbo masu kasuwanci a jihar Arewa sun koka kan yadda ake karbar haraji a hannunsu

Tattalin arzikin Mauritius ya yi nasarar wuce duk yadda gwamnatin kasar ta yi hasashe musamman a bangaren sarrafa sukari da tufafi.

Libya

Duk da kalubalen siyasa da tattalin arziki da ta fuskanta a cikin 'yan kwanakin nan, kasar Libya ta arewacin Afirka tana da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na dala 26.527

Arzikin kasar Libya ya samo asali ne daga dimbin albarkatun mai da take da shi, kuma tana kan kokarin daidaita tattalin arzikinta don gogayya da kasashe masu arziki a Afirka.

Botswana

Yayin da ta ke da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na dala 20.311, an san Botswana da ingantaccen cigaban tattalin arziki ta hanyar dabarar rarraba hanyoyin samun kudaden shiga.

Botswana ta sarrafa albarkatun lu'u-lu'un kasarta yadda ya kamata tare da saka hannun jari a fannin bude ido da noma, da ya ba da gudummawa ga ƙarfin arzikinta.

Gabon

A matsayi na hudu ita ce kasar Gabon da ke yammacin Afrika, wacce ke da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na dala 19,865, kuma ta na da dimbin albarkatun kasa da suka hada da mai da ma'adinai.

Kara karanta wannan

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa za ta binciki gwamnatin Yar'adua, Jonathan da Buhari kan fitar da $496m

Gwamnatin kasar ta jaddada ci gaba mai dorewa da fadada hanyoyin bunkasa tattalin arziki, musamman don rike matsayinta a jerin kasashe mafi arziki a Afrika.

Masar

Babbar kasar da ke a Arewacin Afirka tana matsayi na biyar a jerin tare da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP ana dala 17,786.

Tattalin arzikin Masar ya bambanta, tare da sassa masu mahimmanci da suka haɗa da yawon shakatawa, noma, da masana'antu.

Equatorial Guinea

Tare da dala 17,237 a matsayin jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP, Equatorial Guinea ta dogara kacokan kan dimbin arzikin man da take da shi domin bunkasa tattalin arzikinta.

Har yanzu dai man fetur na taka rawar gani a tattalin arzikin kasar, amma tana kokarin habaka tattalin arzikinta da zuba jari a fannoni daban-daban kamar noma.

Afirka ta Kudu

Kasa ta biyu mafi girma a Afrika ita ce ta bakwai a jerin IMF na kasashe mafi arziki a nahiyar tare da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na dala 16,625.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba MTN, Airtel da Glo umarnin abin da za su yi da layukan da ba su da NIN

Tattalin arzikin Afirka ta Kudu ya ƙunshi hakar ma'adinai, masana'antu, da ayyuka, sai dai kasar na fuskantar kalubale kamar rashin daidaito da rashin aikin yi.

Aljeriya

Ƙasar Ajeriya wacce ke a Arewacin Afirka tana da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na dala 14,227. Ta dogara kacokan a kan sinadarin hydrocarbons, tare da yunƙurin komawa kan makamashi don bunkasa tattalin arzikinta.

Tunisiya

Tunusiya tana da jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na dala 13,695 kuma tana da dabarun bunkasa tattalin arziki a Arewacin Afirka.

Tunisiya ta mai da hankali kan gyare-gyaren tattalin arziki, yawon bude ido, da masana'antu, wanda ke ba da gudummawa ga matsayinta a cikin ƙasashe mafi arziki a Afirka.

Maroko

Jimillar karfin tattalin arzikin kasa da PPP na Maroko a yanzu ya kai dala 10,926. Kasar ta gina tattalin arzikinta daga fannin noma, yawon bude ido, da masana'antu, wanda hakan ya sa take taka muhimmiyar rawa a Afirka.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari kan tsadar rayuwa

Kasashen Afrika 10 da cin hanci da rashawa ke tasiri

A wani labarin, Legit Hausa ta tattaro bayani kan wasu ƙasashen Afrika guda 10 da cin hanci da rashawa ya zame masu ruwan dare.

Yayin da kididdigar CPI na 2023 ya nuna Somaliya ce ke kan gaba a jerin sunayen, ya kuma ruwaito cewa cin hanci na da ɗan sauki sauki a kasar Eritrea.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.