Jerin Kasashen Afrika 10 Masu Ban Mamaki da Cin Hanci da Rashawa Ya Zama Ruwan Dare

Jerin Kasashen Afrika 10 Masu Ban Mamaki da Cin Hanci da Rashawa Ya Zama Ruwan Dare

Bisa kididdigar cin hanci da rashawa ta CPI na 2023, cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a duniya, ba a bar nahiyar Afrika a baya ba.

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Kididdigar ta tantance kasashe da yankuna 180 bisa yadda aka fahimci tafiyar da gwamnati da matakin cin hanci da rashawa a cikinsu.

An ba da maki daga 0 zuwa 100, inda hakan ke nuna mafi muni a rashawa da kuma mafi tsarki a bakin aikin.

Kasashen da suka fi rashawa a Najeriya
An bayyana kasashen da suka fi rashawa a Afrika | Hoto: African Union
Asali: Twitter

Sama da kashi biyu bisa uku na kasashen sun samu maki kasa da 50% cikin 100% a kididdigar ta CPI, sakamakon da ya nuna batutuwan cin hanci da rashawa da dama, in ji Business Day.

Kara karanta wannan

Wasan karshe na AFCON: Gaskiyar batu kan bidiyon da ke zargin golan Ivory Coast da sanya guraye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kuma sun tsaya a 43%, tare da kasashe da dama da ke nuni da cewa babu wani ci gaba ko samun raguwa a cikin shekaru goma da suka gabata.

Sai dai, kusan kasashe 23 sun sami mafi karancin maki a wannan shekara a ma’aunin na cin hanci da rashawa, rahoton Business Insider.

Idan muka duba a kasa, akwai kasashe 10 na Afirka da suka fi fama da cin hanci da rashawa, bisa tsarin kididdiga na CPI na kasa da kasa.

Somaliya - CPI: 11; Matsayi a duniya: 180

Kasar da ke gabashin Afirka ta jagoranci sauran kasashen Afirka zuwa 2024. Cin hanci da rashawa ya yi kamari a kasar saboda tashe-tashen hankulan siyasa da kuma rikice-rikicen da ke faruwa.

Somaliya na da raunin gwamnati, isasshen fada aji da sa ido, da kuma rashin hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da gaskiya da amana a turbar ci gabanta.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

Sudan ta Kudu - CPI: 13, Matsayi a duniya: 177

Kasar mafi karancin shekaru a duniya na fama da cin hanci da rashawa tun bayan da ta samu ‘yancin kai a 2011.

Ana shan gwagwarmayar wahalar wutar lantarki, rashin sarrafa albarkatun kasa yadda ya dace, karkatar da kudade daga muhimman ayyuka da lalata ababen more rayuwa.

Irin wadannan ne suka haifar da manyan kalubale ga ci gaban tattalin arzikin kasar a halin da ake ciki.

Equatorial Guinea - CPI: 17, Matsayi a duniya: 172

Ita ma kasar mai arzikin man fetur na fuskantar kalubalen cin hanci da rashawa, rabuwar kai da wawure dukiyar kasa.

Akwai rashin gaskiya da kuma rashin sarrafa albarkatu masu tarin yawa a kasar, wanda ya yi tasiri ainun kan yadda karfin mulki ke tafiya.

Libya – CPI: 18, Matsayi a duniya: 170

Libya na fama da cin hanci da rashawa, raunin cibiyoyin gwamnati da rashin zaman lafiya a siyasance a tun bayan juyin juya hali da aka samu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Babban jigon cin hanci da rashawa a kasar shi ne hanyar sarrafa arzikin man fetur na kasar.

Hakan ya kara zafafa kalubalen mulki da hana ci gaban tattalin arziki ainun.

Sudan – CPI: 20, Matsayi a duniya: 162

Kasar da ke Arewacin Afirka na da tarihin rudani da kitimurmurar siyasa da tabarbarewar tattalin arziki.

Duk da sauye-sauyen siyasa na baya-bayan nan, har yanzu kasar na fuskantar kalubale na cin hanci da rashawa. Sudan na ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a sassa daban-daban.

Matsalar ta shafi ayyukan gwamnati da kuma karin matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.

DR Congo - CPI: 20, Matsayi a duniya: 162

DR Congo dai kasa ce a Afirka da ke fama da matsalar cin hanci da rashawa a sassan gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu, lamarin da ya kawo cikas ga ci gabanta.

Kasar na da albarkatu masu tarin yawa, amma babban abin da ke kawo cikas ga ci gabanta da ci gaban rayuwar al’ummarta shi ne cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Ma’aikatu da Hukumomi 256 sun yi kaca-kaca da N256bn ba da sanin Gwamnati ba

Comoros - CPI: 20, Matsayia a duniya: 162

Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a tsibirin kuma ya yi tasiri sosai a kasar. Babban abin da ke haifar cin hanci da rashawa a kasar ba komai bane face talauci da rashin daidaito.

Comoros na fuskantar kalubale na samar da ingantacciyar hanya don yaki da matsalar cin hanci da rashawa da inganta gaskiyar tafiyar da lamurra.

Chadi - CPI: 20, Matsayi a duniya: 162

Babban abin da ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasar Chadi shi ne cin hanci da rashawa. Kasar ba ta da ingantaccen makamin yaki da cin hanci da rashawa.

Babu wani ma'aunin da zai iya durkusar da fatara da rashin daidaito a kasar, wanda hakan ya zama babban kalubale ga ci gaban al’umma.

Burundi – CPI: 20, Matsayi a duniya: 162

A Burundi cin hanci da rashawa wani gagarumin shinge ne ga ci gaban kasar da ma al’ummarta. Kalubalen cin hanci da rashawa ta yi tasiri sosai a ga yadda kasar ke tafiya.

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

Cin hanci da rashawa da ake yawan samu a kasar ya kasance babban jigon da ke taimaka wajen ta’azzarar kalubalen da kawo kunci ga mazauna kasar

Eritrea – CPI: 21, Matsayi a duniya: 161

Ana daukar Eritrea a matsayi na 10 a cikin kididdigar cin hanci da rashawa a Afrika yayin da take fama da kalubalen cin hanci da rashawa kan hanyoyinta na neman ci gaba.

Kusan ya zama dole ga kasar ta magance matsalar cin hanci da rashawa domin share fagen samar da kyakkyawar makoma ga al'ummarta.

Me ke jawo karuwar cin hanci da rashawa?

A shekarun baya, ministan sufuri a Najeriya ya taba bayyana hanyar da za a bi don tabbatar da an yaki cin hanci da rashawa a Najeriya.

Rotimi Amaechi ya ce, abin da ke ta'azzara cin hancin ba komai bane face rashin daukar mataki mai tsauri kan wadanda ake kamawa da aikata laifukan.

Sai dai, har a gwamnatin Buhari an samu lokacin da gwamnati ta yafewa gwamnonin da aka tabbatar da 'yan rashawa ne a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel