'Yan Kabilar Igbo Masu Kasuwanci a Jihar Arewa Sun Koka Kan Yadda Ake Karbar Haraji a Hannunsu

'Yan Kabilar Igbo Masu Kasuwanci a Jihar Arewa Sun Koka Kan Yadda Ake Karbar Haraji a Hannunsu

  • Tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya na ci gaba da yin dama-dama da kasar, ya bazu ko'ina a jahohi, lamarin da ke kara tunzura ‘yan kasa
  • Rahotannin baya-bayan nan sun tabbatar da cewa tuni ‘yan kasuwa a jihar Kwara suka fara gudanar da zanga-zanga
  • An tattaro cewa zanga-zangar ta biyo bayan karin haraji da ofishin tattara kudaden shiga na jihar Kwara ya yi a kwanan nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kwara - ’Yan kabilar Igbo da ke kasuwanci a Ilorin, Jihar Kwara, sun nuna damuwa a ranar Juma’a ta hanyar rufe shagunansu domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira cin zarafi da kakaba harajin da ya wuce kima a kansu.

Kara karanta wannan

'Yan daudu sun farmaki ofishin Hisbah a Kano tare da yin fashe-fashe, an gano dalili

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar tattara kudaden shiga ta jihar, ta kara adadin kason harajin da ‘yan kasuwa za su ke biya a jihar.

‘Yan kasuwar, sun umurci mambobinsu musamman a yankunan Taiwo, Agaka, Baboko, Ita-Amodu, da sauran shiyyoyi da mazauna garin Ilorin da su dakatar da harkokin kasuwanci nan take.

'Yan Igbo sun koka kan yadda ake karbar haraji a hannunsu
'Yan kasuwa Igbo a Kwara sun koka kan yawan haraji a kansu | Hoto: Analodu
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da muke samu daga jaridar Punch ya tabbatar da cewa, shaidun gani da ido sun bayyana cewa, tabbas manyan shagunan ‘yan kabilar Igbo a jihar ba a bude su ba a ranar.

Halin da kwastomomi suka shiga a Ilorin

A cewar majiya, wannan lamari ya jawo tsaiko, inda jama’a da yawa suka takura ainun da rashin samun inda za su yi siyayya a yankunan jihar, rahoton AIT.

Da ‘yan kasuwan ke bayyana kokensu, sun ce ma’aikatan haraji kan zo musu da misalin karfe 10 na safe tare da kotun tafi-da-gidanka, inda ake cin zarafinsu da nuna musu wariya.

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

Sun kuma koka kan yadda aka kara musu harajin ya zama yana cinye da yawa daga dan riban da suke samu a hada-hadar kasuwanci na yau da kullum.

Daga nan suka bayyana kokensu ga gwamnati, inda suka nemi gwamnan jihar da ya tsoma tare da tausaya musu ta hanyar rage harajin.

Martanin ofishin harajin Kwara kan ikrarin ‘yan Igbo

Sai dai da ta take martani, hukumar harajin ta bakin Shade Omoniyi ta ce gwamnati ta turo kotun tafi-da-gidanka ne don daukar mataki kan ‘yan kasuwan da ba sa biyan haraji.

Hakazalika, hukumar ta bayyana shirinta na ci gaba da daukar matakin da ya dace kan wadanda ba sa biyan hakkin gwamnati da ke kansu.

Akan samu sabani tsakanin ‘yan kasuwa a jihohi daban-daban na Najeriya, musamman yadda ake ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki.

Bukatar NLC a zanga-zangar da ta yi

Rahoton da muka samu shi ne kungiyar NLC ta fadawa shugaba Bola Tinubu a shigo da abinci da siminti da sauran kaya daga kasar waje.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun fito zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Arewa

'Yan kwadago suna so a fasa karin kudin makaranta, a cire VAT kuma a daina karbar haraji a hannun ma’aikata saboda an shiga kunci.

Tun bayan hawan Bola Tinubu mulki 'yan kasar ke kukan tsadar rayuwa da kuma bakin talauci da ke ci gaba da addabar 'yan kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel