Yanzu-yanzu: FG ta tsige shugaban TCN

Yanzu-yanzu: FG ta tsige shugaban TCN

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsige manajan daraktan Hukumar Rarrabe Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN)

- Kamar yadda wasikar da ta fito daga kakakin ministan wutar lantarki, Aaron Artimas ta bayyana, Mohammed Sale ya amince da wannan sallamar a ranar Talata

- Har ila yau, a wasikar aka bada umarnin cewa Injiniya Sule Ahmad ya maye gurbinsa a matsayin mukaddashin manajan daraktan hukumar

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sallama manajan daraktan Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN).

Ministan wutar lantarki, Mohammed Sale ne ya amince da sallamar a ranar Talata inda ya nada Sule Abdulaziz don aiki a matsayin mukaddashin shugaban.

"Daga cikin kokarin kawo gyara da saita fannin wutar lantarki na kasar nan, ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman yake sanar da manyan sauye-sauye a kamfanin rarrabe wutar lantarki na Najeriya," Aaron Artimas, kakakin ministan ya sanar a wata takarda.

DUBA WANNAN: Gambari ya ajiye mukaminsa a SCDDD

"An tsige manajan daraktan TCN, Usman Gur Mohammed daga kujerarsa a take. An maye gurbinsa da Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz a matsayin mukaddashin manajan daraktan.

"Mai girma ministan ya sake tabbatar da nadin wasu daraktoci hudu da suke aiki a matsayin mukaddasan daraktoci a kamfanin na wani lokaci," ya kara da cewa.

A lokacin da Injiniya Mamman ya hau mukamin watanni takwas da suka wuce, an ba shi wasu hanyoyin kawo gyara a fannin wutar lantarkin kasar nan.

Kamar yadda yace, ma'aikatarsa za ta tashi tsaye wajen tabbatar da ta kawo karshen rashin nasarorin da ake samu tare da tabbatar da cikar burikan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce fannin wutar lantarki koyaushe yana zama wani jigon samar da ci gaba tare da tabbatar da sabbib tsare-tsaren ci gaba na kowacce kasa.

A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Kwara ta yi rashin wakilin ta da Shugaba Buhari ya zaba domin nada shi mamba a Hukumar Daidaito a Ayyukan Gwamnatin Tarayya (FCC), James Kolo.

Marigayi Kolo ya rasu ne a ranar Talata a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Ilorin (UITH) bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel