Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Tabarya Har Lahira a Jihar Ribas

Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Tabarya Har Lahira a Jihar Ribas

  • Wani matashi ya yi ajalin mahaifinsa saboda ya hana shi kuɗin da ya nema a jihar Ribas ranar Alhamis
  • Ganau ya bayyana cewa da alamu yaron ya sha kwayoyinsu kuma bayan aikata laifin ya yi kokarin guduwa amma mutane duka cafke shi
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da lamarin inda ta ce tuni ta kama wanda ake zargi kuma ta miƙa kes din sashin bincike

Rivers - Wani matashi mai suna Ikechi ya haddasa tashin hankali yayin da ya halaka mahaifinsa ta hanyar amfani da Taɓarya a Rumuaghaolu da ke ƙaramar hukumar Obio Akpor a jihar Ribas.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa matashin ya tafka wannan ɗanyen aiki ne bayan ya nemi mahaifinsa ya ba shi kuɗi, amma ya ƙi, bisa haka ya yi ajalinsa.

Taswirar jihar Ribas.
Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Tabarya Har Lahira a Jihar Ribas Hoto: punchng
Asali: UGC

An ce Ikechi ya fusata bayan mahaifin ya nuna ba zai ba shi kuɗin da ya nema ba, nan take ta rarumo Taɓarya ya buga masa a kai, daga bisani kuma rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Taya Shugaba Tinubu Murnar Samun Nasara a Kotu? Gaskiya Ta Bayyana

Yadda lamarin ya faru tun farko

Wani ganau ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya auku ne da tsakar rana ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya bayyana cewa matashin ya fusata matuƙa bisa rashin samun abinda yake so daga wurin uban, ya tafi ya ɗauko Taɓarya ya maka masa a kai kuma nan take a wurin mahaifin ya mutu.

Shaidan da abun ya faru a idonsa ya ce:

"Ya fusata sosai kan marigayin ya ki ba shi kudin da ya nema jiya a Road 9, Rumuagholu a Patakwal, babban birnin jihar Ribas."
“Ana zargin matashin yan shawo ƙwayoyinsa, ya tambayi babansa kudi ya ƙi ba shi, kawai ya dauki taɓarya ya buga masa."

A cewarsa, yaron ya yi ƙoƙarin guduwa daga wurin bayan ya fahimci ɗanyen aikin da ya aikata amma mutane suka riƙe shi.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Dawo Da Albashin Da Gwamnati Ta Rika Biyan Mahaifinsa Bayan Ya Rasu a Kano, Gwamna Ya Yi Masa Wani Muhimmin Abu

Wane mataki 'yan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tunk yan sanda suka kama wanda ake zargin.

“Eh, zan iya tabbatar da faruwar lamarin. An kama yaron kuma an miƙa kes ɗin sashen binciken masu aikata manyan laifuka."

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wurin Ibada, Sun Kashe Malami a Kaduna

A wani labarin na daban 'Yan bindiga sun sake kai hari kan wata majami'a a Fadan Kamantan yankin Kafanchan da ke kudancin jihar Kaduna.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun banka wuta a ɗaya daga cikin gidajen da ke ƙarƙashin Cocin, lamarin da ya yi ajalin mutum ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262