CBN: Babban Banki Ya Soke Lasisin Ƴan Canji Sama da 4,000, Ya Faɗi Muhimmin Dalili

CBN: Babban Banki Ya Soke Lasisin Ƴan Canji Sama da 4,000, Ya Faɗi Muhimmin Dalili

  • Babban banki CBN ya soke lasisin ƴan canji sama da 4,000 a wani ɓangare na kokarin dawo da martabar Naira kan Dala a Najeriya
  • Daraktan yaɗa labarai na CBN, Sidi Ali Hakama, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juumu'a, 1 ga watan Maris, 2024
  • Sanarwan ta kara da cewa an soke lasisin ne saboda sun gaza kiyaye wasu tanade-tanaden doka da ƙa'idojin harkar canjin kuɗi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya ci gaba da ɗaukar matakai kan ƴan kasuwar canjin kuɗi (BDC) a ƙoƙarin farfaɗo da darajar Naira ranar Jumu'a.

A wannan karon, CBN ya soke lasisin aikin ƴan canji 4,173 kuma hakan na ƙunshe a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Twitter.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya yun yi luguden wuta kan ƴan ta'adda, sun tura da dama lahira

CBN ya soke lasisin ƴan canji a Najeriya.
Babban Banki CBN Ya Soke Lasisin Ƴan Canji Sama da 4000 a Najeriya Hoto: CBN
Asali: Facebook

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun kakakin CBN, Sidi Ali Hakama, ta ce babban bankin ya ɗauki wannan matakin ne bisa la'akari da ƙarfin ikon da doka ta ba shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa CBN ya soke lasisin ƴan canji?

Sanarwar ta ce:

"Duba da karfin ikon da doka ta ba shi a kundin harkokun banki da hada-hadar kuɗi (BOFIA) ta 2020, sashi na 5 da ƙa'idojin dokar canjin 2015, CBN ya soke lasisin ƴan canji 4,173.
"Jerin ƴan canjin da aka soke masu lasisi na nan a shafin yanar gizo na babban bankin ƙasa. Dukkan waɗanda matakin ya shafa sun gaza kiyaye akalla ɗaya daga cikin tanadin doka kamar haka:
"Na farko biyan duk kuɗaɗen da suka wajaba, gami da sabunta lasisi a cikin lokacin da aka kayyade daidai da ƙa'idojin da aka gindaya."
"Sai kuma kiyaye ƙa'idoji, umarni da jadawalin CBN, musamman dokokin hana safarar kudi, dakile tallafawa ta'addanci da bada gudumuwar barkowar makamai.

Kara karanta wannan

Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ya yi murabus, ya faɗi dalili

- Sidi Ali Hakama

Karin bayanin Kakakin bankin CBN

CBN ya ƙara da cewa a halin yanzu yana kara nazari kan ƙa'idojin ayyukan ƴan canji da kuma sanya wa harkokinsu ido domin tabbatar da komai na tafiya kan hanya.

Babban bankin ya kuma jaddada cewa biyayya ga sababbin matakan da aka ɗauka zai zama tilas ga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin da zaran sun fara aiki.

Gwamnan CBN ne ya jawo tsadar rayuwa?

A wani rahoton kuma Gwamnan CBN ya nesanta kansa daga hannu a jefa ƴan Najeriya cikin wannan halin na yunwa da matsin tattalin arziki.

Olayemi Cardoso ya bayyana cewa shi da tawagarsa ba su suka jawo tsadar rayuwa ba, amma zasu yi duk mai yiwuwa don shawo kan komai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel