An Tarwatsa Masu Zanga-Zanga Kan Harin ‘Yan Bindiga a Jihar Arewa

An Tarwatsa Masu Zanga-Zanga Kan Harin ‘Yan Bindiga a Jihar Arewa

  • Jami'an tsaro sun tarwatsa wasu fusatattun mutane da suka toshe babban titin Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga
  • A safiyar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, ne mutanen garin Gonin Gora a karamar hukumar Chikun, suka mamaye titin saboda harin da 'yan bindiga suka kai masu
  • Masu zanga-zangar sun sanya shinge kan titin wanda hakan ya haifar da cunkoson ababen hawa, inda matafiya suka yi cirko-cirko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kaduna - Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun tarwatsa fusatattun masu zanga-zanga da suka tare babban titin Kaduna zuwa Abuja a yau Alhamis, 29 ga watan Fabrairu.

Majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta kuma gargadi masu zanga-zangar kan toshe hanyoyi da cin zarafin bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da sunan zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun fito zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar Arewa

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Kaduna
An Tarwatsa Masu Zanga-Zanga Kan Harin ‘Yan Bindiga a Jihar Arewa Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Matasan dai sun yi zanga-zanga ne don nuna fushinsu kan harin da 'yan bindiga suka kai Unguwan Auta a Gonin Gora, karamar hukumar Chikun. Zanga-zangar ta kuma hana matafiya samun hanya, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da kwamishinan ma'aikatar tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya saki, ya ce mambobin majalisar tsaron sun tarwatsa shingayen da aka kafa, daga bisani kuma suka bude hanyar domin masu motoci.

Aruwan ya kara da cewa a lokacin da suke zantawa da shugabannin al’umma, mambobin majalisar tsaro na jihar sun nuna rashin gamsuwarsu da barazanar da ke tattare da toshe hanyoyi.

Sun ce yin hakan tauye hakkin ‘yan kasa da matafiya da ke amfani da hanyoyin ne.

Jami'an tsaro na bibiyar maharan, Aruwan

Aruwan ya kuma bayyana cewa jami’an tsaron da suka isa unguwar a cikin daren sun yi artabu da ’yan bindigar wanda a dalilin haka suka samu nasarar kubutar da wasu daga cikin wadanda aka sace, rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda Kanawa suka karade titunan Kano a zanga-zangar kin jinin tsadar rayuwa

Har ila yau, ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bibiyar sahun 'yan bindigar domin daukar mataki a kansu.

Aruwan ya ce:

"A daidai lokacin wannan karin bayani na tsaro, 'yan kasa da masu motoci na bin yankin Gonin Gora na hanyar Kaduna-Abuja ba tare da cikas ba."

'Yan bindiga sun tarwatsa garuruwa 10

A wani labarin, mun kawo a baya cewa miyagun ƴan bindiga sun tarwatsa mutanen kauyuka alal aƙalla 10 a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, mazauna garuruwan sun tarwatse sun bar gidajensu ne saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel