"Bashi Muke Biya": Shehu Sani Ya Bayyana Ainahin Wanda Ya Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Mawuyacin Hali
- Sanata Shehu Sani ya magantu kan halin da ake ciki na matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a Najeriya
- Tsohon 'dan majalisar tarayyar, ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jefa 'yan Najeriya a halin da suke ciki a yanzu
- Sani ya kuma ce Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da 'yan Najeriya kudirinsa na aiwatar da manufofinsa tun kan ya hau mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya lalata tattalin arzikin Najeriya, tare da jefa 'yan Najeriya a halin da suke ciki na matsin rayuwa.
Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels TV, a shirin Politics Today a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu.
A fadi illar da Kiripto ke yi wa tattalin arziki yayin da aka cafke shugabannin Binance, za a haramta
Abin da ya kamata Buhari ya yi da yake mulki, Sani
Tsohon 'dan majalisar tarayyar, ya bayyana cewa kamata ya yi ace Buhari ne ya aiwatar da wasu daga cikin manufofin tattalin arziki da Tinubu ya aiwatar a yanzu, wadanda sune suka haifar da matsin tattalin arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Sani ya ce tsohon shugaban kasar ya ki aiwatar da manufofin, wanda hakan ya sa tattalin arzikin kasar ya tabarbare, rahoton Vanguard.
Sani ya ce:
"Dole mu zama masu fada wa kanmu gaskiya, matsalar da muka tsinci kanmu a ciki a yau, ta samo asali ne daga gwamnatin Buhari.
"Gwamnatin Buhari ta lalata tattalin arzikin Najeriya sosai."
Tinubu bai yaudari 'yan Najeriya ba, tsohon sanatan Kaduna
Sani ya wanke Tinubu kan halin da ake ciki a yanzu, yana mai cewa, tun a lokacin yakin neman zabe ya bayyana cewa zai aiwatar da manufofin, don haka bai yaudari 'yan Najeriya ba.
Ya ce:
"Lokacin da Tinubu ya karbi mulki, ya san cewa babu tallafin mai kuma magana ta gaskiya, ya fito fili ya fadi gaskiya a lokacin yakin neman zabensa. 'Zan cire tallafin mai kuma duk zanga-zangar da zai biyo bayansa ba zan janye ba' kuma mutane suka zabe shi, don haka bai yaudari 'yan Najeriya ba.
"Yanzu yana kan mulki, muna biyan bashin kuskuren da aka yi a baya ne, na kin yin abin da ya kamata mu yi a baya, don haka wannan ne zahirin gaskiya."
Tinubu ya ba 'yan Najeriya hakuri
A wani labarin, mun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu, a ranar Laraba, ya roki ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki, inda ya ba da tabbacin cewa sauƙi na nan tafe.
Shugaban ya ce yana da cikakkiyar masaniya kuma ya ɗauki alhakin matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng