Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Nadin Dan Uwan Sarkin Bichi, Salisu Ado Bayero

Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Nadin Dan Uwan Sarkin Bichi, Salisu Ado Bayero

  • Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da masarautar Bichi daga naɗa Salisu Ado Bayero sarautar Hakimin Bichi "saboda wasu dalilai"
  • A cikin wata sanarwa da kwamishinan kananan hukumomi na jihar ya aike wa masarautar Bichi, gwamnatin ta ce dakatarwar ta nan take ce
  • A ranar 15 ga watan Fabrairu ne masarautar Bichi ta rubutawa Salisu Ado Bayero wasika na a nada shi a matsayin hakimin gundumar Bichi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta umarci majalisar masarautar Bichi da ta dakatar da bikin nadin sarautar Salisu Ado Bayero a matsayin hakimin masarautar.

Salisu kane ne ga Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An karrama sojoji 8 da suka ƙi karbar cin hancin naira miliyan 1.5 daga hannun ɓarayin shanu

Gwamnatin Kano ta dakatar da nadin Salisu Ado Bayero.
Wasu dalilai sun saka gwamnatin Kano ta dakatar da nadin Salisu Ado Bayero.
Asali: Twitter

Mataimakin gwamna kuma kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi, Kwamared Aminu Abdulsalam ne ya bayyana haka a wata wasika da ya aikewa sakataren masarautar Bichi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi, Ibrahim M Kabara, ta ce akwai bukatar dakatar da nadin “saboda wasu dalilai."

Lokacin da aka shirya nadin Salisu Ado Bayero

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne Masarautar Bichi ta rubutawa Salisu Ado Bayero wasika inda ta sanar da shi amincewar sarkin na a nada shi a matsayin hakimin gundumar Bichi.

Wasikar ta umurci Yariman da ya zo fadar a ranar Juma'a 1 ga watan Maris domin yi masa rawani a matsayin hakimin gundumar.

Sakataren Masarautar Ibrahim Yakasai, lokacin da aka tuntubi shi bayan karbar wasikar, ya ce a tuntubi ma’aikatar kula da kananan hukumomin inda wasikar ta fito.

Kara karanta wannan

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa za ta binciki gwamnatin Yar'adua, Jonathan da Buhari kan fitar da $496m

Gwamnatin Kano na mutunta sarakuna

Sai dai babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba ya bayyana cewa tsarin da aka kafa ya bukaci masarautun su rubuta tare da neman izini kafin a yi wani nadi.

Ya ce babu wata kiyayya ga kowane sarki domin irin wannan umarni an bai wa sauran masarautun jihar, inda ya ce mataimakin gwamnan yana mutunta ubannin sarauta.

Ibrahim Garba ya yi nuni da cewa wasikar da aka aikewa Masarautar Bichi na dakatar da bikin nadin sarautar wani abu ne na al'ada.

Kungiyoyi na neman a mayar da Sanusi II kan karaga

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu kungiyoyi na ta kiraye-kirayen neman a rusa sabbin masarautu tare da maido da hambararren Sarki Muhammadu Sanusi.

Wata kungiya mai suna ‘Yan Dangwallen Jihar Kano a ranar 16 ga watan Fabrairu ta aike da sakon tunatarwa ga majalisar dokokin jihar inda ta bukaci ta duba dokar tsige Sarkin Kano.

Ta nemi majalisar da tamayar da Sanusi II kan karagar mulki tare da rusa sabbin masarautun Gaya, Rano, Bichi da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel