Hawan Sallah: Hakimai 11 sun yi watsi da umarnin Ganduje, sun yi biyayya ga sarki Sanusi II

Hawan Sallah: Hakimai 11 sun yi watsi da umarnin Ganduje, sun yi biyayya ga sarki Sanusi II

Wasu hakimai 11 da suka fada arkashin sabbin masarautun da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kirkira sun halarci hawan Sallah na yammacin ranar Litinin a masarautar sarkin birnin Kano, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.

Sun halarci hawan na 'Daushe' ne sabann umarnin da gwamnatin Kano ta fitar a kan cewa kowanne hakimi ya halarci hawa Sallah a karkashin sabon sarkin masarautarsa.

Hakiman da suka kauracewa umarnin Ganduje tare da yin biyayya ga sarkin Kano, Sanusi II, sune; Madakin Kano; Yusuf Nabahani (hakimin Dawakin Tofa), Dan Amar; Aliyu Harazimi Umar (hakimin karamar hukumar Doguwa), Muhammad Aliyu (hakimin Garko), Makama; Sarki Ibrahim (hakimin Wudil), sarkin fulani; Ja'idinawa Buhari Muhammad (hakimin karamar hukumar Garin Malam, da Barde; Idris Bayero (hakimin karamar hukumar Bichi).

Ragowar sune; Sarkin Bai; Adnan Mukhtar (hakimin karamar hukumar Danbatta), Yarima Lamido Abubakar (hakimin karamar hukumar Takai), Dan Isa; Kabiru Hashim (hakimin warawa), Dan Madami; Hamza Bayero (hakimin karamar hukumar Kiru) da Sarkin Dawaki Mai Tuta; Bello Abubakar (hakimin karamar hukumar Gabasawa).

DUBA WANNAN: Sallah: Buhari ya yanka ragonsa na layya a Daura (Hoto, bidiyo)

A wani jawabi da, Abba Anwar, kakakin gwamna Ganduje ya fitar ranar Lahadi, gwamnatin Kano ta bukaci Hakiman da su yi watsi da umarnin sarkin Kano na su zo birnin Kano domin gudanar da hawa tare da umartarsu da su gudanar da hawa a karkashin sabbin masarautunsu.

Umarnin gwamnatin jihar ya saba wa sanarwar da fadar masarautar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta fitar, inda ta gayyaci dukkan hakiman jihar Kano da su halarci hawan Daushe, wanda aka saba yi kwana daya da Sallah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng