Tsadar Rayuwa: Mutanen Abuja Sun Koma Ga Awara a Madadin Nama
- Wata mata da ke sana'ar awara a yankin Bwari, babban birnin tarayya, ta magantu kan yadda take samun kwastamomi a baya-bayan nan
- Hannatu Musa, ta ce mutanen Abuja sun koma cin amara a abinci a madadin nama saboda tsadar da ya yi
- 'Yan Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Abuja - Wata mai sana'ar awara a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya, Misis Hannatu Musa, ta bayyana cewa mutane da dama sun koma ga awara a madadin nama.
Hannatu, wacce ta zanta da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Bwari, ta ce tun bayan da nama ya yi tsada, sai wasu suka koma ga amfani da awara a madadin shi.
Matar ta bayyana cewa awara na da matukar farin jini musamman a Arewacin kasar saboda dadinsa da kuma sinadaren da yake tattare da shi masu kara lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na samu karin kwastamoni, Hannatu mai awara
Ta bayyana cewa ta samu karin kwastamomi a yan baya-bayan nan, saboda mutane sun gane cewa ana iya cinsa a madadin nama, musamman ma a bangaren masu neman sauki.
Jaridar Vanguard ta nakalto matar tana cewa:
"Daya daga cikin kwastamomina ya fada mani cewa yana siyawa ahlin gidansa baki daya don su kara kan abincinsu.
"Tun da ba zan iya siyan nama ko kifi ba akai-akai yanzu kuma yarana suna sonasa, shi yasa na maye gurbin nama da shi."
Sai dai kuma, ta ce duk da amfanin awara ga lafiya, sarrafa shi na da matukar cin lokaci da wahala, wanda shine dalilin da yasa mutane ke siyan wanda aka riga aka sarrafa.
Likita ta fadi alfanun da ke tattare da awara
Dr Kemi Adegoke-Abraham, kwararriya a fannin abinci, ta ce abincin da aka yi da waken suya, yana da tarin sinadarin bitamin da karancin 'carbohydrates' wanda zai amfani masu cutar sikari.
Legit Hausa ta zanta da wata mazauniyar Abuja don jin yadda suke fama da rayuwa a irin wannan lokaci.
Hajiya Hussai ta ce:
"Ai halin da ake ciki yanzu babu abin da za mu ce sai dai innalillahi wa'inna illaihi raji'un. Talaka ya ga ta kansa, kai yanzu hatta masu rufin asiri suna jin jiki. Toh da wanne mutum zai ji, da babu kudi ko kuma tsadar abin da za a saka a bakin salati.
"Wa ke daka ta nama ma a yanzu, idan har ka samu abinci ka ci ka koshi yanzu ai sai hamdala, don dai shine abin da ke nema ya gagari mutane. A halin da muke ciki a yanzu ko kayan miya aka bar mutum da shi an gama.
"Karamin bokiti na attarugu 4000 ake siyar da shi ka ga kuwa an kai inda ba a cewa komai. Muna dai rokon Allah ya kawo mana sauki a wannan kasa tamu.
Ma'aikaciyar banki ta rungumi sana'ar kiwo
A wani labarin kuma, mun ji cewa wata mata 'yar Najeriya wacce ta bar aiki a matsayin ma'aikaciyar banki ta rungumi noma ta ja hankalin mutane da dama da labarinta.
Wani 'dan gajeren bidiyo na sana'ar kiwon da take yi ya yi bayanin cewa ta mayar da gidanta ya zama wajen da take kiwon kifi da kaji lokacin annobar Korona, wanda ya yi sanadiyar yi wa mutane kulle.
Asali: Legit.ng