Abin Tausayi Yayin da Fitacciyar Mawakiya a Najeriya Ta Ce Ta Na Daf da Makancewa, Ta Magantu

Abin Tausayi Yayin da Fitacciyar Mawakiya a Najeriya Ta Ce Ta Na Daf da Makancewa, Ta Magantu

  • Shahararriyar mawakiya a Najeriya, Tiwa Savage ta bayyana yadda ta ke fuskantar matsalar makanta
  • Savage ta ce ta shafe fiye da shekaru uku yanzu ta na fama da matsalar wacce ke neman hana ta gani karfi da yaji
  • Mawakiyar ta fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafin Instagram inda ta ce da fama da matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Fitacciyar mawakiya a Najeriya, Tiwa Savage ta bayyana irin jarabawar da hadu da ita a ‘yan kwanakin nan.

Tiwa Savage ta ce ta na daf da makancewa bayan shan fama da ta ke yi na rashin gani sosai a yanzu.

Fitacciyar mawakiya ta bayyana babban matsalar da ta ke fuskanta
Fitacciyar Mawakiya, Tiwa Savge Ta Ce Ta Na Daf da Makancewa. Hoto: Tiwa Savage.
Asali: Instagram

Mene Savage ke cewa kan matsalar?

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ba laifin Tinubu ba ne, Igboho ya yi martani kan kalaman Sarkin Musulmi

Ta ce ta shafe fiye da shekaru uku yanzu ta na fama da matsalar wacce ke neman hana ta gani karfi da yaji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafin Instagram, fitacciyar mawakiyar ta ce da zaran ta zo karatu ganin nata kara dusashewa ya ke.

Ta ce matsalar karuwa ya ke a ‘yan watannin nan inda ta ce ba ta iya karanta sakon waya musamman idan kanana ne.

Ta bayyana yadda lamarin ya ke mata

A cewarta:

“Cikin shekaru biyu zuwa uku ina fahimtar wasu abubuwa wanda duk lokacin da nake karatu sai gani na ya dusashe.
“A cikin ‘yan watannin nan naga abin kara muni ya ke yi saboda ko karatu sai na matso da su kusa nake karantawa.
“Lokacin da na ke Landan na je wurin likita saboda ina ganin daga nesa amma duk abin da ya ke kusa ba na iya ganinsa.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta raba kayan tallafi ga talakawan Najeriya, minista ya yi karin bayani

Tiwa ta ce ko da gidan cin abinci ta ziyarta ba ta iya karanta jerin kayan abincin da ya kamata na siya.

Jarumar fina-finai ta rasu

A baya, kun ji cewa fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.

Jarumar ta rasu ne bayan fama da cutar daji na tsawon lokaci a ranar 11 ga watan Faburairun wannan shekara da muke ciki.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke ya rasu a jihar Ogun bayan fama da jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel