Dalar Amurka: Naira Ta Tashi a Kasuwar Canji a Sakamakon Dabarun Cordoso a CBN
- A ‘yan kwanakin baya-bayan nan, Naira ba ta rasa darajarta ba, sai dai aka ji kudin Najeriyan yana kara kima
- Jama’a sun ce tun da dai Dalar Amurkar tana fadi ne a kan kudin Najeriya, ya kamata farashin kaya su sauko
- A halin yanzu kaya sun yi tsada kasuwanni da sunan Dala ta tashi, hakan ya sa gwamnan bankin CBN ya tashi tsaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A farkon makon nan aka ji labari Naira ta cigaba da tashi a kasuwar canji, idan aka kamanta farashinta da Dalar Amurka.
Rahoto ya zo daga The Cable cewa Naira ta dawo N1, 650 a kan kowace Dala a kasuwar bayan-fage da aka fi sani da kasuwar canji.
Dala ta sauka a kan Naira a BDC
Naira ta tashi da fiye da 6% a ‘yan kwanakin nan, ma’ana Dalar Amurka ta rasa sama da N100 daga karshen makon jiya zuwa yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan za a tuna, a ranar Juma’ar da ta gabata, an saida kowace Dalar Amurka kan N1, 770 bayan farashin ya sauka a tsakiyar wata.
‘Yan kasuwar canji da ke Legas sun yi wa Dala farashi a kan N1, 650 idan mutum zai saida, masu saye kuwa suna biyan N1, 600.
A halin yanzu, ribar N50 ‘yan canji suke samu a kan kowace Dalar kasar Amurka a Legas bayan wani mugun tashi da Dala tayi.
Masu sana’ar saida kudin ketare sun tabbatar da farashin yana sauka, amma suna tsoron zai iya tashi idan dai Dala tayi wahala.
Naira ta doke Dala a bankuna
A bankuna kuwa, rahoton ya ce Dala ta kara daraja da kusan 5% domin a maimakon N1, 665, an saida $1 jiya ne a kan N1,582.94/$.
Bayanan da aka samu daga kafar FMDQ Exchange ya tabbatar da haka a ranar Litinin kamar yadda jaridar ta tabbatar dazu.
CBN ya saki $300m a bankuna
An samu sauki ne bayan wasu tsare-tsare da dokokin da CBN ya kakabawa ‘yan canji kuma Punch ta ce an saidawa bankuna $300m.
Dalolin da babban bankin ya saidawa bankunan kasuwa ya taimaka wajen rage karancin kudin, hakan yana nufin farashi zai sauko.
Naira za ta hau kan Dala
Rahoton nan ya ce Mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro yana so a gangaro da farashin Dalar Amurka da sauran kudin ketare.
Malam Nuhu Ribadu yana aiki da CBN, ‘yan sanda, kwatsam da NFIU domin a farfado da kimar Naira da aka rasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng