Babban Abin Kunya: An Kama Matashi da Laifin Sace Motar Surukinsa, Ya Siyar N230,000

Babban Abin Kunya: An Kama Matashi da Laifin Sace Motar Surukinsa, Ya Siyar N230,000

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda aka kama wani matashi da zargin sace motar surukinsa a Ogun
  • An ruwaito cewa, tuni ya shiga hannun jami’an tsaro, kuma ya yi kokarin ba da cin hanci don a sake shi
  • Ba wannan ne karon farko da ake kame matasa da aikata munanan ayyukan laifi na sata ba, hakan ya sha faruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Ogun - An kama wani matashi dan shekara 27 mai suna Fatai Sholola da laifin satar mota mallakin mijin ‘yar uwarsa tare da siyar da ita akan kudi Naira 230,000.

Wasu jami’an So-Safe Corps ne suka kama Sholola a Sango ta karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Yan daba sun yi yunƙurin kutsawa kasuwar Jos don satar kayan abinci, jami'an tsaro sun dauki mataki

Kakakin So-Safe, Moruf Yusuf, ya tabbatar wa wakilin jaridar Punch kamen matashin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

An kama matashi da laifin sace motar surukinsa
Abin kunya ya faru, matashi ya shiga hannu bayan sace motar surukinsa | Hoto: So-Safe Corps
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kama matashin da laifin sace mota?

A cewar Yusuf, sun kama Sholola da misalin karfe 2:00 na safe yayin da jami’an rundunar ke sintiri a kusa da Sango Plaza a ranar Juma’a.

Yusuf ya naqalto kwamandan So-Safe na jihar yana cewa:

“’Yan sintiri sun binciki jakar da yake rike da ita, kuma sun ga takardun mota a hannunsa, amma ya kasa bayyana dalilin da ya sa yake dauke da wadannan takardu.”

An ce wanda ake zargin ya yi yunkurin bai wa jami’an cin hancin Naira 30,000, amma suka ki amincewa, Osun Defender ta ruwaito.

Dama ana neman matashin ruwa a jallo kan sata

Ya kara da cewa:

“Abin takaici bayan titsiye shi an gano ya saci mota ne kuma takardun da ke hannunsa na motar da ya sace ne.”

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar EFCC sun cafke ɗaliban jami'ar Arewa, sun aikata wani babban laifi

An kuma ruwaito cewa, tuni an alanta neman wanda ake zargin ruwa a jallo tun kwanaki sama da takwas da suka gabata.

A halin da ake ciki dai ana ci gaba da bincike kan tushen lamarin tare da daukar matakin da ya dace na doka.

Majinyaci ya saci motar asibiti a Kano

A wani rahotonmu na baya, kun ji yadda wani majinyaci ya tattaro karfinsa ya sace motar asibiti a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

Wannan lamari dai ya faru ne da wani mutumin da ke jinyar karayar kafa a wani asibitin da ke birnin mai cunkoson jama'a.

Daga baya, an bayyana yadda 'yan sanda suka kama mutumin a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa mai makwabtaka da Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.