Kano: Tashin Hankali Yayin da Mummunar Gobara Ta Ɓarke a Kasuwar Ƴan Katako, an Samu Karin Bayani
- Mummunar gobara ta tashi a kasuwar ƴan katako da ke Rijiyar Lemo, karamar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano
- Gobarar ta tashi da misalin karfe 2 na safiyar ranar Litinin, inda ta lakume shaguna 21 da ke a bangaren ƴan hada kayan ɗaki
- Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ce ta sanar da hukumar kashe gobarar halin da ake ciki, inda aka kashe gobarar tare da dakile yaduwarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kumbotso, Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta kone shaguna 21 a kasuwar 'yan katako da ke Rijiyar Lemo a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Kakakin hukumar Saminu Abdullahi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 02:00 na safiyar ranar Litinin.
Ba a yi asarar rayuka ba - Hukumar kashe gobara
Premium Times ta ruwato Malam Abdullahi na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 02:00 na safe daga hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) cewa an samu tashin gobara a kasuwar 'yan katako.
“Mun yi gaggawar tura jami’an mu zuwa wurin da lamarin ya faru, inda muka kashe gobarar tare da dakile ta daga bazuwa zuwa wasu shaguna.”
Hukuma na binciken musabbabin tashin gobarar
Mista Abdullahi ya ce akalla shagunan 21 ne gobarar ta shafa da ke a bangaren hada kayan daki na kasuwar.
Ya ce ba a rasa rai ba, kuma hukumar na kan binciken musabbabin tashin gobarar, kuma za ta fitar da cikakken rahoto da zaran an kammala bincike.
Gobara ta tashi a ofishin 'yan sanda na jihar Kano
A wani labarin makamancin wannan, mummunar gobara ta babbake wani bangare na ofishin 'yan sandan Kano da ke karamar hukumar Nasarawa.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Husaini Gumel ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce gobarar ta tashi a safiyar Litinin.
Ba wannan ba ne karo na farko da ofishin 'yan sandan Kano ke kamawa da wuta ba, inda a farkon shekarar 2024 wuta ta kaka a hedikwatar ƴan sanda ma Bompai.
Asali: Legit.ng