Rayuka 7 Sun Salwanta Saboda Turmutsitsi a Wajen Siyan Shinkafar Kwastam a Jihar APC

Rayuka 7 Sun Salwanta Saboda Turmutsitsi a Wajen Siyan Shinkafar Kwastam a Jihar APC

  • Jam'iyyar APC a jihar Legas ta yi alhinin mutuwar daya daga cikin mambobinta a FKL Ward E1, Misis Comfort Adebanjo
  • Misis Adebanjo da wasu mutane shida sun rasa rayukansu a ranar Juma'a sakamakon turmutsitsi da aka samu wajen siyan shinkafar kwastam
  • Hukumar kwastam dai ta sanar da fara siyarwa 'yan kasa da shinkafar da ta kwace kan farashi mai rahusa, domin ragewa talakawa radadin halin da ake ciki na tsadar rayuwa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Lagos - Jam'iyyar APC ta tabbatar da mutuwar daga daga ciki mambobinta, Comfort Adebanjo, da wasu mutum shida a wajen siyan shinkafar da hukumar kwastam ke siyarwa don rage tsadar rayuwa a kasar.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, jam'iyyar mai mulki ta tabbatar da hakan ne a wani sakon ta'aziyya da ta saki a ranar Asabar, domin alhinin wadanda suka rasu.

Kara karanta wannan

Murna ta ɓarke yayin da gwamnan APC ya fara siyar da shinkafa kan farashi mai rahusa ga talakawa

Hukumar kwastam ta fara siyar da shinkafa mai rahusa
Rayuka 7 Sun Salwanta Sakamakon Turmutsitsi a Wajen Siyan Shinkafar Kwastam a Jihar APC Hoto: @CustomsNG
Asali: Twitter

Jaridar Legit ta rahoto a baya cewa hukumar kwastam ta sanar da shirinta na siyarwa talakawan Najeriya kayan abincin da suka kwace, kan farashin mai rahusa don rage radadin halin da ake ciki a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta sanar da siyarwa 'yan Najeriya da suka mallaki katin shaidar 'yan kasa na NIN buhun 25kg na shinkafa kan N10,000.

Yadda turmutsitsi ya yi ajalin mutum 7 a Legas

Sai dai kuma, an samu turmutsitsi a ranar Juma'a, wajen siyar da kayan abincin, wanda ya yi sanadiyar rasa ran mutum bakwai, rahoton Politics Nigeria.

Shugaban FKL Ward E1, na jam'iyyar APC a jihar Legas, Oluwafemi Fadahunsi, da sakatarensa, Kwamrad Adebari Adewale, sun tabbatar da cewar Adebanjo na daya daga cikin mutum bakwai da suka mutu yayin turmutsitsin.

A sakon ta'aziyya da ta saki a ranar Asabar, jam'iyyar ta ce:

Kara karanta wannan

25kg kan N10k: Kwastam ta fara siyar da shinkafa a farashi mai rahusa, ta fadi inda za a samu

"Cike da nauyin zuciya da danasani muke sanar da mutuwar daya daga cikin mambobinmu a FKL WARD E1, Misis Adebanjo Comfort Funmilayo, ta gida mai lamba 104, unguwar Ibidun ta AKINHANMI, Ojuelegba.
"Tana cikin mutum 7 da suka mutu a yayin siyarnshinkafar kwatsam a Yaba.
"Allah Ubangiji ya bai wa daukacin ahlin gidanta da dukkan mazauna WARD E1 juriyar wannan babban rashi."

Fadar shugaban kasa ta magantu kan rabon abinci

A wani labarin kuma, mun ji cewa a ranar Juma’ar nan fadar shugaban kasa ta sanar da inda aka kwana game da alkawarin raba metric ton 42, 000 na hatsi.

Mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya sanar da wannan a wani jawabi da ya fitar a Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel