Dubu ta cika: An Kama Ɗaliban Fitacciyar Jami'ar Arewa Bisa Zargin Kashe Rayukan Bayin Allah

Dubu ta cika: An Kama Ɗaliban Fitacciyar Jami'ar Arewa Bisa Zargin Kashe Rayukan Bayin Allah

  • Yan sanda sun kama ɗalibai 2 na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi bisa zargin suna da hannun a kisan mutum biyu
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmad Wakil, ya ce sun kuma kama ƙarin wani mutum ɗaya mai alaka da kisan
  • Ya bayyana cewa a halin yanzu suna ci gaba da bincike domin gano sauran abokansu da suka aikata wannan aika-aika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Jami'an ƴan sanda sun cafke wasu ɗaliban jami'ar Abubakar Tafawa Balewa ATBU Bauchi, Hoomvez Martins Nyelong, da Daniel Audu Adamu.

Dakarun ƴan sandan sun kama matasan ɗaliban ne bisa zargin yin sanadin mutuwar wasu mutum biyu a kauyen Durum mai maƙotaka da ɗakunan ɗalibai na Gubi.

Kara karanta wannan

Jama'a sun daka wa tirelar kayan abinci wawa a jihar Katsina? An gano gaskiyar abinda ya faru

Yan sanda sun kama ɗaliban jami'ar ATBU Bauchi.
Yan sanda sun kama ɗaliban jami'ar ATBU Bauchi Bisa Zargin Kisan Rayuka Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Bayan haka ƴan sanda sun cafke ƙarin mutum ɗaya, Maigari Inuwa, wanda ya yi ikirarin ya gama digiri a jami'ar Jos, bisa zargin yana da alaka da kisan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukkan waɗanda aka kama da wannna zargin mambobin ƙungiyoyin asiri ne, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmad Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a wata sanarwa ranar Juma’a.

Taya ɗaliban ATBU suka aikata kisa

Ya ce wani mazaunin kauyen Durum ne ya sanar da jami’an ‘yan sanda na ofishin ‘C’ bayan gano gawarwakin mutanen da aka jefar a daji a wurare daban-daban.

Kakakin ƴan sandan ya ce an kai gawar ɗaya cikin mutanen da aka kashe mai suna Reheboth Joseph Deshi, amma ɗayan ba a iya gano ainihin bayanansa ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa a jihar Arewa

A rahoton Daily Post, ya ce:

"An ga wadanda ake zargin suna yawo a yankin, sannan da aka kama su kuma sun kasa bayar da gamsasshen bayani kan abinda suke yi a yankin.
“Haka nan da aka duba gawarwakin biyu ba a ga wani alamar rauni ko tashin hankali ko shakewa ba. Amma idanun jikin na karshe da aka gano an huda su da karfi."

Wakil ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, jami'ai sun kara zage damtse da nufin gano matsugunansu tare da damke sauran abokansu.

Gwamnan Lawal ya je kauyukan da aka kai hari

A wani rahoton kuma Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyara ta musamman yankunan da ƴan bindiga suka kai hari a kananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara.

Yayin wannan ziyara, gwamnan ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da jaddada shirin gwamnati na dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel