Tsadar Rayuwa: Duk da Gargadin 'Yan Sanda, Mummunar Zanga-zanga Ta Barke a Legas, Bayanai Sun Fito

Tsadar Rayuwa: Duk da Gargadin 'Yan Sanda, Mummunar Zanga-zanga Ta Barke a Legas, Bayanai Sun Fito

  • Da safiyar yau Litinin ce 26 ga watan Faburairu aka barke da zanga-zanga a jihar Legas kan halin da ake ciki a kasar
  • Zanga-zangar na zuwa ne bayan gargadin da kwamishinan 'yan sanda a jihar ya yi a jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu
  • hukumar kare hakkin dan Adam mai suna 'Take it Back Movement' ta fito zanga-zangar kan tsadar kayan abinci a Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Duk da barazana daga jami'an tsaro, jama'a sun barke da zanga-zangar don nuna damuwa kan halin da ake ciki a Legas.

Wata hukumar kare hakkin dan Adam 'Take it Back Movement' ta fito zanga-zangar kan tsadar kayan abinci a jihar Legas, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Yan Najeriya sun sako jarumar fim a gaba kan kamfen a zabi Tinubu, ta shiga damuwa

Zanga-zanga ta sake barkewa kan halin kunci da ake ciki
Mutane sun fito zanga-zanga ce don nuna rashin jin dadi kan halin kunci. Hoto: Daniel Chibuzo.
Asali: Twitter

Menene dalilin fitowa zanga-zangar a Legas?

Wannan na zuwa ne bayan jami'an tsaro sun yi gargadi kan fitowa zanga-zangar a fadin kasar duk da halin kunci da ake ciki, Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Adegoke Fayoade a jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu ya yi gargadi kan gudanar da zanga-zangar.

Masu zanga-zangar na rike da takardu da ke dauke da rubuce-rubuce na nuna rashin jin dadi kan tsadar kayayyaki, cewar The Nation.

An gano jami'an tsaro a wurin zanga-zangar

An gano jami'an 'yan sanda a wurin zanga-zangar don tabbatar da dakile tashin hankali a yayin gudanar da zanga-zangar.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan irin wannan zanga-zanga ta barke a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.

Daga bisani zanga-zangar ta sake fashewa a jihohin Kano da Oyo da kuma Cross River Kan tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun cafke wasu dattawa 2 da kokarin sace kanin gwamnan PDP, sun shiga ha'ula'i tun yanzu

Zanga-zanga ta barke a Neja kan halin kunci

A baya, kun ji cewa Mazauna birnin Minna da ke jihar Neja sun fito zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan tsadar rayuwa a kasar.

Mutanen sun fito zanga-zangar ce a ranar Litinin 5 ga watan Faburairu inda suka cika titunan birnin.

Wannan ya biyo bayan halin da 'yan kasar ke ciki na mawuyacin hali da matsin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel