BBC Ya Lissafo Kwanakin da Tinubu Ya Shafe a Turai Cikin Watanni 9, An Kwatanta da Buhari

BBC Ya Lissafo Kwanakin da Tinubu Ya Shafe a Turai Cikin Watanni 9, An Kwatanta da Buhari

  • An kwatanta adadin kwanakin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya shafe a turai cikin watanni tara a ofis da na magabacinsa, Muhammadu Buhari
  • Rahoton BBC ya ce Tinubu ya shafe kwanaki 71 a wajen Najeriya cikin watanni tara kacal, yayin da magabacinsa, Buhari, ya shafe kwanaki 59 a wajen Najeriya a lokacinsa
  • Rahoton BBC ya yi bayanin cewa koda dai abokin adawa, Atiku Abubakar, ya caccaki Tinubu, shugaban kasar na bukatar yin tafiyan don kulla yarjejeniya da karfafa diflomasiyya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani rahoton BBC ya kwatanta tafiye-tafiyen Shugaban kasa Bola Tinubu cikin watanni tara da kama aiki da na magabacinsa, Muhammadu Buhari.

A watan Janairu, babban abokin hamayya Atiku Abubakar ya caccaki Shugaba Tinubu lokacin da ya sake tafiya Turai a wani ziyarar kashin kai.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Yadda Buhari ya tura DSS don su kashe ni, Sunday Igboho ya yi zargi

Tinubu ya fi Buhari fita waje a watanni taran farko a ofis
“Yawale”: BBC Ya Lissafo Kwanakin da Tinubu Ya Shafe a Turai Cikin Watanni 9, An Kwatanta da Buhari Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Atiku ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya don cewa Najeriya bata bukatar “babban mai yawon bude ido”, inda ya kara da cewa kasar na nutsewa cikin tekun rashin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, rahoton BBC ya bayyana wannan sukar a matsayin mara tasiri, cewa shugaban kasar na bukatar halartan wasu tarukan shugabannin kasashe da karfafa alakar kasashen waje.

Baya ga dalilai na diflomasiyya, akwai batun tattalin arziki da za a yi la'akari da shi. Hakan ya faru ne saboda kasancewar wannan lokaci ne da ake tattaunawar zuba hannun jari masu riba.

Sau nawa Tinubu ya yi tafiya a cikin watanni tara?

A bisa ga rahoton BBC, Tinubu ya yi akalla tafiye-tafiye 14 zuwa kasashen waje cikin watanni takwas da kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Haka kuma ya ce sauran shugabannin duniya ma sun kara yawan tafiye-tafiyensu zuwa kasashen waje, amma Tinubu ne ya fi shan suka.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da malamin Musulunci ya nemi a kashe matar Tinubu

Daga nan ne sashin labaran ya bayyana adadin kwanakin da Tinubu ya yi a wajen kasar nan, idan aka kwatanta da na magabacinsa, Buhari a cikin watanni tara na farko a kan karagar mulki.

Alkaluma na BBC sun nuna cewa Tinubu ya kwashe kwanaki mafi yawa a kasashen waje idan aka kwatanta da Buhari a cikin watanni tara na mulki.

A cikin watanni tara, Tinubu ya shafe kwanaki 71 a wajen Najeriya, yayin da Buhari ya kwashe kwanaki 59 lokacin da yake kan mulki.

ECOWAS ta dage takunkumin da ka kaƙabawa Jamhuriyar Nijar

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Shugaba Bola Tinubu ke yi wa jagoranci ta dage takunkumi kan daya cikin mambanta, Jamhuriyar Nijar.

An rahoto cewa an dauki wannan matakin ne yayin taron shugabannin kungiyan kasashen Afirka ta Yamman da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi, 24 ga watan Fabrairu, kan dalilan jin kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel