Aisha Buhari Ta Ce Ainahin Mijinta Ya Rasu a 2017? Gaskiya Ta Bayyana

Aisha Buhari Ta Ce Ainahin Mijinta Ya Rasu a 2017? Gaskiya Ta Bayyana

  • An yi ta yada jita-jita a shafukan soshiyal midiya cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya mutu a 2017
  • Buhari ne shugaban kasar Najeriya na 15 kuma shine ya mika mulki ga shugaban kasa mai ci, bayan ya yi shugabanci daga 2015 zuwa 2023
  • Wani dandalin binciken gaskiya ya gudanar da bikice kan ikirarin cewa matar Buhari ta tabbatar da mutuwar tsohon shugaban kasar a 2024

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Daura, jihar Katsina - An yi wani ikirari kwanan nan cewa matar tsohon shugaban kasa, Aisha, ta magantu game da zargin da ke kewaye da mijinta, Muhammadu Buhari.

Rahoton da wani shafin yanar gizo, Igbo Times Magazine ya wallafa, ya yi ikirarin cewa Aisha ta ce Buhari ya mutu a shekarar 2017 a kasar Ingila.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Yadda Buhari ya tura DSS don su kashe ni, Sunday Igboho ya yi zargi

Bincike ya nuna Aisha bata ce Buhari ya mutu a 2017 ba
Aisha Buhari Ta Ce Ainahin Mijinta Ya Rasu a 2017? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Rahoton ya nakalto Aisha na cewa an biya wani mutumin kasar Sudan wanda ke kwaikwayon halayyar mutane kudi don ya dunga yin abubuwa kamar tsohon shugaban Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wallafar na cewa:

"Ainahin mijina Buhari ya mutu a 2017 a kasar Ingila kafin aka biya wani mutumin kasar Sudan wanda ke kwaikwayon halayyar mutane kudi don ya dunga yi kamar marigayi mijina - Aisha Buhari matar tsohon shugaban kasa ta magantu."

Jaridar Legit ta rahoto cewa an yi ta yada jita-jita a soshiyal midiya cewa an maye gurbin Buhari da wani mutum mai suna "Jubril" daga Sudan.

A bisa ga binciken dandalin gano gaskiyar lamari na AFP Fact Check, jita-jitar ta fara ne a karshen 2017 kuma ya bayyana a dandalin Facebook, X da YouTube.

'Yan aware sun kara rura wutar jita-jitar, kamar yadda masu binciken gaskiyar suka gano.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da malamin Musulunci ya nemi a kashe matar Tinubu

Har yanzu rahoton mutuwar Buhari kanzon kurege ne

A wani rahoto a ranar Juma'a, 23 ga watan Fabrairu, wani dandalin bincike don gano gaskiya, Africa Check, ya ce ya kimanta wasu ikirari na mutuwar Buhari a 2019 da 2020 a matsayin karya.

Africa Check ya ce:

"Babu wani hujja cewa Buhari ya mutu yayin da yake shugabancin kasa sannan aka maye gurbinsa da mai kama da shi.
"Idan aka yi la'akari da yanayin yaduwar wannan ikirari, da kafafen watsa labarai na gida da waje sun kawo rahoton furucin da matar tsohon shugaban kasar ta yi cewa mijinta ya rasu a 2017.
"Sai dai kuma, babu wani sahihin kafar yada labarai na cikin gida ko na waje da suka ruwaito cewa ta yi irin wadannan kalamai.
"Ikirarin na ta yawo a yanar gizo tun 2017. Kuma dai karya ce a 2024."

Tinubu ya tura sako ga Aisha Buhari

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya tura sakon murna ga matar tsohon shuaban kasa, Muhammadu Buhari.

Tinubu ya tura sakon murnar ce don taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarta shekaru 53.

Asali: Legit.ng

Online view pixel