Qatar Ta Yi Fatali da Bukatar Tinubu Don Wata Ganawa Mai Muhimmanci a Kasar? Gaskiya Ta Fito Fili

Qatar Ta Yi Fatali da Bukatar Tinubu Don Wata Ganawa Mai Muhimmanci a Kasar? Gaskiya Ta Fito Fili

  • Yayin da ake ta yada jita-jitar cewa Qatar ta ki amincewa da ganawa da Tinubu, ma’aikatar kasashen waje ta yi martani
  • Ma’aikatar ta musanta rahoton da ake yadawa inda ta ce Tinubu zai ziyarci kasar a ranar 2-3 ga watan Maris
  • A rahoton da ake yadawa an ce Qatar ta yi fatali da shirin ganawa da Tinubu kan wasu dalilai masu karfi a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ma’aikatar kasashen waje ta yi martani kan rade-radin cewa Qatar ta ki amincewa da bukatar Tinubu don wata ganawa.

Ma'aikatar ta musanta rahoton da ake yadawa inda ta ce Tinubu zai ziyarci kasar a ranar 2-3 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 bayan nasarar Kwankwaso a kotu, uban NNPP ya nemi hadin kai kan abu 1 game da Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan zargin Qatar ta yi watsi da bukatar Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta karyata cewa Qatar ta yi watsi da bukatar Tinubu don wata ganawa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Menene ma'aikatar ke cewa?

Ma’aikatar kasashen wajen ita ta yi wannan martani a yau Asabar 24 ga watan Faburairu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan an yada cewa hukumomi a Qatar sun yi fatali da bukatar Tinubu don ganawa kan zuba hannun jari a kasar, cewar Arise TV.

Rahoton ya ce Qatar ta ki amincewa da bukatar shugaban don ganawa kan harkokin kasuwanci da Najeriya a ranar 2-3 ga watan Maris.

Sanarwar ta ce:

“Kasar Qatar ta na tunatar da ma’aikatar kasuwanci a Najeriya cewa ba za ta iya ganawar ba saboda wasu matsaloli.
“Abin takaici babu wani yarjejeniya tsakanin Qatar da kuma Najeriya kan zuba hannun jari da kasuwanci.”

Martanin ma'aikatar kan jita-jitar

Sai dai ma’aikatar kasashen waje a Najeriya ta bakin Minista Yusuf Tuggar ta ce tabbas Tinubu zai ziyarci kasar Qatar.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Yan Najeriya sun sako jarumar fim a gaba kan kamfen a zabi Tinubu, ta shiga damuwa

Sanarwar ta ce:

“Ma’aikatar kasashen waje ta tabbatar cewa Tinubu zai ziyarci kasar Qatar a ranar 2-3 ga watan Maris.
“Ziyarar za ta kunshi tattaunawa kan harkokin kasuwanci da tattalin arziki da abin da ya shafi diflomasiyya.”

Ma’aikatar ta ce ta na sane da labarin da ke yawo cewa Qatar ta soke tattaunawa da kasar Najeriya saboda wasu dalilai.

NNPP ta roki ‘yan Najeriya kan Tinubu

A wani labarin, jam’iyyar NNPP ta tura roko ga ‘yan Najeriya kan taya addu’a ga Tinubu don shawo kan matsalolin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan kasar na cikin wani hali da ke neman jawo matsala ga gwamnatin Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.