Jama'a Sun Daka Wa Tirelar Kayan Abinci Wawa a Jihar Katsina? An Gano Gaskiyar Abinda Ya Faru

Jama'a Sun Daka Wa Tirelar Kayan Abinci Wawa a Jihar Katsina? An Gano Gaskiyar Abinda Ya Faru

  • Hukumar ƴan sanda ta jihar Katsina ta fayyace gaskiya kan bidiyon da ke yawo na yadda mutane suka daka wa tirelar abinci wawa a jihar
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce bincike ya nuna babu wani abu mai kama da haka da ya faru a kewayen Katsina
  • Ya kuma gargaɗi al'umma da su gujewa yaɗa jita-jita irin wannan domin za ta iya haifar da tashin hankali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta musanta rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa wasu mazauna jihar sun daka wa motar abinci wawa.

Rundunar ta bayyana wani faifan bidiyo da ake yaɗawa wanda ya nuna jama'a na ɗibar ganima a wata tirela makare da kayan abinci a matsayin na ƙarya.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ɗaliban fitacciyar jami'ar Arewa bisa zargin kashe rayukan bayin Allah

Sufetan yan sanda na ƙasa.
Yan sanda sun musanta bidiyon daka wa motar abinci wawa a jihar Katsina Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ƴan sandan Katsina ta wallafa a shafinta na manhajar X watau Twitter ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan, mai magana da yawun ƴan sandan, ASP Abubakar Aliyu, ya ce a binciken da suka gudanar sun gano cewa babu wani abu makamancin haka da ya afku a faɗin Katsina.

A kalamansa ya ce:

"Babu wata shaida da ke tabbatar da cewa jama'a sun farmaki motar tirela maƙare da kayayyakin abinci kuma sun daka mata wawa a faɗin jihar nan kamar yadda bidiyon ya yi iƙirari."
"Saboda haka muna mai tabbatar wa al'umma cewa wannan jita-jitar gaba ɗayanta karya ce mara tushe."

Wace illa yaɗa bayanan karya ka iya haifar wa?

Kakakin rundunar ƴan sandan ya roƙi daukacin ƴan Najeriya da su gujewa yaɗa labaran da ba su tabbatar da ingancinsu ba domin kauce wa illar da zai iya haifarwa a tsakanin al'umma.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

A cewarsa, irin waɗannan bayanan na ƙarya ka iya tada yamutsi a tsakanin mutanen jihar Kastsina ko ƙasa baki ɗaya.

Aliyu ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, Mista Aliyu Musa, ya jajirce wajen daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da doka da oda a jihar.

Sojoji sun samu galaba kan masu garkuwa da mutane

A wani rahoton na daban kun ji cewa Sojojin rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu babbar nasara a wani samame da suka kai kan ƴan bindiga a jihar Benuwai.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya ce dakarun sun yi nasarar ceto mutane 12 da aka yi garkuwa da su a hanyar kai su Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel