Tsadar Rayuwa: Wanka da Bahaya Ya Yi Tashin Gwauron Zabo a Jihar Arewa, An Gano Dalili

Tsadar Rayuwa: Wanka da Bahaya Ya Yi Tashin Gwauron Zabo a Jihar Arewa, An Gano Dalili

  • Yayin da abubuwan ke ƙara tsada a Najeriya, masu gidan wanka da bahaya a jihar Bauchi sun kara kuɗin amfani da wurarensu da kaso 100
  • Shugaban ƙungiyar masu gidan bahaya na Bauchi, Ibrahim Kabo, ya ce ƙarin ya zama tilas saboda kayan da suke amfani da su wajen tsafta sun tashi
  • A yanzu wanka ko bahaya sun tashi daga N100 zuwa N200 kan kowane mutum ɗaya, sannan sun ƙarawa ma'aikatansu albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Ƙungiyar masu gidan wanka da bahaya a ƙaramar hukumar Bauchi ta sanar da ƙarin kaso 100% watau nunka kuɗin amfani a wuraren kasuwancinsu.

Shugaban ƙungiyar, Ibrahim Kabo, shi ne ya sanar da nunka kuɗin a wata hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Alhamis a Bauchi.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Farashin dala zai faɗi warwas a Najeriya nan ba da daɗewa ba, gwamna ya magantu

Masu gidan wanka da bahaya a Bauchi sun kara kuɗi.
Tsadar Rayuwa: Wanka da Bahaya Sun Yi Tashin Gwauron Zabi a Jihar Bauchi Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Ya bayyana cewa sun kara kuɗin bahaya zuwa N200 daga N100 da ake biya a baya yayin da kuɗin wanka da ruwan ɗumi ko na sanyi ya koma N200.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka ƙara kuɗin bahaya a Bauchi?

Mista Kabo ya bayyana cewa an samu wannan karin ne sakamakon tsadar kayayyakin da suke amfani da su wajen kulawa da gidajen wanka da bahaya.

Daily Nugerian ta tattaro a jawabinsa yana cewa:

"Muna amfani da sabulun wanka, maganin kashe kwayoyin cuta, man fetur, bokiti, tsintsiya, kwandon shara, takardar bayan gida da sauransu don tsaftace wuraren wanka da bahaya ga jama'a.
“A daya bangaren kuma, mun kara kudin sufuri ga ma’aikatan mu sabida rawar da suke takawa na da matukar muhimmanci domin su ne ke kula mana da kayan aiki.
"Wannan shi ne musabbabin da ya jawo tashin farashin amfanin da gidan wanka da bahaya a kwaryar birnin Bauchi."

Kara karanta wannan

Murna yayin da aka fadi lokacin kawo karshen 'yan bindiga a jihar Arewa

Ya ce a matsayinsu na masu fafutukar kawo karshen bahaya barkatai a fili, dole ne su kara yawan kudaden domin su iya biyan bukatunsu da kuma ci gaba da kasuwanci.

Ya mutane suka ji da karin?

Da yake martani kan ƙarin, wani kwastoma mai suna Sani Ɗanjuma, ya ce ƙarin ba shi da daɗi amma sun fahimci dalilin masu gidan wanka.

"Banga laifinsu ba da suka kara kuɗi saboda komai ya tashi, dan haka ba zai yiwu mu yi tunanin samun sauƙin kuɗin bahaya ba," in ji shi.

Meke faruwa a asibitin sojojin Najeriya?

A wani rahoton kuma Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa akwai wata sabuwar cuta da ta ɓulla a asibitin soji na 44 NARHK da ke Kaduna.

Rundunar ta ce cutar ta kashe ma'aikatan lafiya guda uku tare da majinyacin da ake fargabar shi ne ke dauke da cutar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel