Aisha Buhari Ta Yi Sabuwar ‘Yar Jikalle, Matar Tinubu da Shettima Sun Je Barka

Aisha Buhari Ta Yi Sabuwar ‘Yar Jikalle, Matar Tinubu da Shettima Sun Je Barka

  • Oluremi Tinubu, uwargidan Shugaban kasa Bola Tinubu ta ziyarci matar tsohon shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari
  • Oluremi ta ziyarci tsohuwar takwarar tata ne domin yi mata barkar 'karuwar da suka samu na 'yar jikalle
  • Zahra Buhari da mijinta, Ahmed Indimi sun haifo kyakkyawar diyarsu mace inda aka sanya mata Aisha wato dai takwarar kakarta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta ziyarci matar tsohon shugaban kasa, Aisha Buhari, wacce ta samu 'yar jikalle.

Zahra Buhari, matar Ahmed Muhammad Indimi ce ta haifo diya mace inda aka sanya mata sunan kakarta, Aisha.

Oluremi Tinubu ta ziyarci Aisha Buhari da jikarta
Aisha Buhari Ta Yi Sabuwar ‘Yar Jikalle, Matar Tinubu da Shettima Sun Je Barka Hoto: @SenRemiTinubu
Asali: Twitter

Oluremi ta samu rakiyar matar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Shettima a yayin ziyarar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An nemi Shugaban Ƙasa Tinubu ya tsige wasu ministoci kan muhimmin abu 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata wallafa da ta yi a shafinta na X, a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu, uwargidar shugaban kasar ta ce Aisha Buhari da diyarta sun dawo gida don kula da jinjirar.

Ta rubuta a shafin nata:

“Abin farin ciki ne a gare ni da uwargidan mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Shettima da muka kasance a gidan matar tsohon shugaban kasar Najeriya, mai girma Dakta A’isha Buhari don yi mata maraba da dawowa gida bayan zama da 'yarta don kula da sabuwar jikarta.
"Allah ya albarkaci sabuwar jinjirar, iyayenta da kakanninta."

Haka kuma, surukar Zahra, Rahma Indimi ta wallafa bidiyon taron sunan a shafinsa na Instagram.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Remi Tinubu ta ziyarci matar marigayi Akeredolu

A gefe guda, mun kawo a baya cewa Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba, ta ziyarci iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano ya raba gari da Shugaba Tinubu kan tsige 'dan Arewa daga muhimmin mukami

Remi Tinubu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ta isa gidan Akeredolu dake Jerico da misalin ƙarfe 12:45 na rana tare da mataimakin gwamnan jihar Oyo, Bayo Lawal da wasu manyan baƙi.

Matar shugaban kasa ta ja hankalin masu kudi

A wani labarin kuma, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa ba za a iya bayyana Najeriya a matsayin matalauciyar kasa ba duk da halin da ake ciki, inda ta yi kira ga masu kudi da su taimakawa talakawa.

A sakonta na Kirsimeti bayan wani dan kwarya-kwaryan taron Kirsimeti da ta shiryawa yaran gidan marayu na Nana Berry da ke Abuja, Oluremi ta ce shekarar 2024 za ta zamo mai cike da alfahari ga yan Najeriya, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel