Gwamnati Za Ta Fara Raba Kyautan Kudi ga Talakawa Miliyan 12, Minista
- Gwamnatin tarayya za ta bi gidaje ta raba kudi ga talakawa ganin yadda farashin kayan abinci suka tashi
- Ministan kudi da tattalin arziki, Mista Wale Edun ya ce an shirya dawo da tsarin inganta rayuwar marasa galihu
- Dama gwamnatin Bola Tinubu tayi alkawarin za ta rika raba N8000 ga talakawa miliyan 12 na wasu watanni
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ganin halin kunci da masifa da aka shiga a ayuwa, gwamnatin tarayya za ta farfado da bada kyautar kudi ga marasa hali.
Rahoton The Nation ya ce za a zakulo wadanda suka fi kowa talauci da rashin galihu, a taimaka masu da kudi domin su samu sauki.
Talauci ya cinye tasirin tallafin gwamnati
Zuwa yanzu akwai mutane kusan miliyan uku da suke amfana da irin wadannan tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta saba fito da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai hauhawar farashin kaya da kunci ya sa ba a jin tasirin kokarin da gwamnati take yi, wannan ya jawo zanga-zanga a garuruwa.
Talakawa miliyan 12 za su samu kudi
Yanzu gwamnatin Mai girma Bola Ahmed Tinubu ta shirya kara yawan wadanda su ke amfana da tsarin, za a tallafi wasu marasa hali.
Akalla talakawa miliyan 12 za a rika bi har gida a raba masu kyautar tsabar kudi kai-tsaye, yunkurin da mutane suka soka kwanaki.
Albishirin Ministan kudi ga talakawa
Ministan tattalin arzikin Najeriya, Wale Edun ya shaida haka a wajen wani taro da ma’aikatarsa ta shiya a garin Uyo a Akwa Ibom.
Da yake bayanin a ranar Laraba, Wale Edun ya ce za su samu shugaban kasa da nufin ya amince a dawo da tsarin rabon kudi a kasar.
Kwamitin shugaban kasa da ke kula da tsare-tsaren inganta rayuwar marasa galihu ne za su yi wannan zama da mai girma Bola Tinubu.
Adadin talakawa sun karu a Najeriya
Rahoton ya ce ministan kudin yana ganin da bukatar a fadada tsarin domin adadin wadanda suke shan wahala ya karu a yanzu.
Idan aka ba talaka kudi a hannunsa, gwamnati tana ganin wannan zai rage talauci.
Ana kukan cewa akwai rashin gaskiya a tsare-tsaren, Edun ya ce wannan karo za a yi aiki da fasahar zamani domin gyara lamarin.
...ba zai yi tasiri ba inji masani
Dr. Usman Bello yana da digirin PhD a fannin tattalin arziki, a zantawarsa da Legit, ya nuna da wahala kudin da za a raba ya yi tasiri.
Masanin tsimi da tattalin ya ce kyau gwamnati ta hada kai da 'yan kasuwa, sai a raba katin kudi wanda za a iya sayen kaya da shi.
Idan aka yi haka ne za a iya gane yadda aka batar da kudin, kuma wannan zai tabbata mutane ba su kashe wadannan kudi a iska ba.
An rabawa gwamnoni N30bn?
Rahoton da bai tabbata ba ya zo cewa a watannin baya-bayan nan an ba kowane Gwamna N30bn da nufin a taimakawa talakawa.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi ikirarin kowace jiha ta samu kudi ta FIRS saboda kuncin rayuwan da aka fada.
Asali: Legit.ng