Yunwa: An ‘Rabawa’ Gwamnoni Karin Naira Biliyan 30 Kwanan Nan - Shugaban Majalisa

Yunwa: An ‘Rabawa’ Gwamnoni Karin Naira Biliyan 30 Kwanan Nan - Shugaban Majalisa

  • Godswill Akpabio ya taimaka wajen yada rade-radin cewa an rabawa gwamnoni karin kudi da nufin ganin bayan wahalar da ake ciki
  • Shugaban majalisar dattawa ya ce labari maras tabbas ya zo masa game da yadda kowace jiha ta samu N30bn ta hannun hukumar FIRS
  • Kwanakin baya aka fitar da wadannan biliyoyin kudi idan maganar da tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya yi ta tabbata gaskiya ce

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi ikirarin gwamnonin jihohi sun samu kudi a dalilin kuncin da aka shiga.

Dazu Premium Times ta rahoto Godswill Akpabio yana bayanin cewa kowane gwamna a kasar ya karbi N30bn daga asusun tarayya.

Kara karanta wannan

Bayan yunwa ta nakasa mutane, Gwamna a Arewa ya sake fitar da shinkafa don marasa karfi, an bi tsari

Godswill Akpabio
Gwamnoni: Godswill Akpabio a Majalisa Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Shugaban majalisa ya tona asirin gwamnoni?

Shugaban majalisar ya ce an bada wadannan makudan kudi ne domin gwamnoni su magance matsalar yunwa da tsadar abinci da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan zancen na sa ya tabbata, ya kamata a yi amfani da biliyoyin ne wajen ganin an rage tasirin hauhawan farashin kaya a kasuwanni.

Majalisar tarayya tayi zama a ranar Laraba

Shi kan shi Godswill Akpabio ya nuna babu tabbacin wannan labari da yake cewa ya ci karo da shi, domin ba a hukumance ya ji labari ba.

A zaman da majalisa tayi a yau Laraba ne shugaban sanatocin ya bijiro da wannan kishin-kishin, yake cewa duka jihohi sun samu kudi.

Gwamnoni sun samu karin N30bn a kan N2bn

Baya ga N2bn da gwamnatin tarayya ta ba gwamnoni aro, Akpabio ya ce an jihohi sun samu karin wasu N30bn daga hannun FIRS.

Kara karanta wannan

Sanatoci za su kafa kwamitin binciken Buhari kan bashin N30tr da ya ci a CBN

"Dole in bayyana cewa akwai rahoton da bai tabbata ba da ya ce a ‘yan watannin bayan nan, kowace gwamnatin jiha ta samu karin N30bn daga FIRS"
"...daga wajen kason da suke samu daga asusun tarayya domin a taimaka masu su magance matsalar karancin abinci."

- Godswill Akpabio

An rahoto Akpabio ya ce gwamnoni suna da rawa sosai da za su taka, ya nanata zargin cewa suke da iko da kananan hukumominsu.

Tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya yi kira ga gwamnatocin jihohi suyi amfani da kudin yadda ya dace domin yunwa ta ragu a yankinsu.

Majalisa za ta binciki Buhari?

Bankin CBN ya ba gwamnatin tarayya aron kimanin N30tr, rahoto ya zo cewa majalisar dattawa za ta binciki yadda aka kashe kudin.

‘Yan majalisar dattawan kasar sun ce za su yi bincike kan bashin N10tr da aka ba manoma da cinikin kudin kasar waje da aka yi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel