Asirin Malamin Addini Ya Tonu Bayan Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya, Akwai Dalili

Asirin Malamin Addini Ya Tonu Bayan Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya, Akwai Dalili

  • Dubun wani fitaccen Fasto ta cika bayan kama su da zargin yin fashi da makami a birnin Akure da ke jihar Ondo
  • Ana zargin Fasto Adewale Adelu da wasu mutane biyar kan yin fashi a bankuna biyu da ke Akure da kuma Idanre a jihar
  • Daga nan ne alkalin kotun ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya ga kowannensu bayan karanto korafe-korafen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wani fitaccen Fasto da wasu mutane biyar a jihar Ondo.

Wanda ake tuhuma Fasto Adewale Adelu ana zarginsa da sauran mutane biyar da fashi da makami, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun cafke ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Kano

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan malamin addini
Alkali Ya Yi Hukunci Kan Malamin Addini Saboda Zargin Fashi da Makami. Hoto: Federal High Court.
Asali: UGC

Mene ake zargin Faston da aikatawa?

An zargin Faston da sauran ne da yin fashi a bankin Akure da kuma Idanre a ranar 19 ga watan Nuwamba da 8 ga watan Disambar 2011.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda aka yanka hukuncin tare sun hada da Ikechuckwu Maduagwu da Fayemi Olubusuyi da Ropo Adeleye da Dele Otopka da Bayo Omotosho.

Wadanda ake zargin sun kai farmaki bankin Diamond tare da sace kudi miliyan 30 da wayoyi da sauran abubuwan masu amfani.

Har ila yau, sun yi fashi a First Bank a yankin Idanre inda suka sace miliyan hudu da sauran kayayyaki, Punch ta tattaro.

Wane hukunci alkalin kotun ya yanke?

Mai Shari'a, Yemi Fasanmi shi ya yanke hukuncin inda ya ce mai gabatar da kara ya ba da hujjoji gamsassu, cewar Tribune.

Alkalin ya ce duk da babu wani shaidan gani da ido kan laifukan, amma yadda suka furta aikata laifuka ya zama hujja a gare su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya, sun tafka mummunar ɓarna a jihar Arewa

Daga nan ne sai alkalin kotun ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya ga kowannensu bayan karanto korafe-korafen.

Fasto ya bai wa 'yan kasa hakuri

Kun ji cewa wani fitaccen Fasto a Najeriya, Mustapha Solomon ya roki 'yan kasar da su kara hakuri da halin da ake ciki.

Faston ya ce wannan halin kunci da ake ciki na wucin gadi ne kuma zai wuce kamar ba a yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel