Gwamnatin Kano Ta Dauki Sabon Mataki Kan Rumbunan Masu Boye Abinci da Aka Rufe

Gwamnatin Kano Ta Dauki Sabon Mataki Kan Rumbunan Masu Boye Abinci da Aka Rufe

  • Bayan rufe rumbunan ajiya da ake zargin ana ɓoye kayan abinci a cikinsu don su yi ƙaranci, gwamnatin Kano ta ɗauki matakin sake buɗe su
  • Shugaban hukumar karɓar.ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar, ya tabbatar da buɗe rumbunan ajiyan guda 10
  • Muhuyi Magaji ya bayyana cewa rufe rumbunan ya jawo farashin kayayyaki sun yi ƙasa bayan ƴan kasuwa sun fito da kayayyaki suna sayarwa jama'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bayyana a ranar Talata cewa ta buɗe wasu rumbunan ajiya guda 10 da aka rufe.

Hukumar ta rufe rumbunan ajiyan ne dai a makon da ya gabata bisa zargin ɓoye kayayyakin abinci.

Kara karanta wannan

Kwamandojin ƴan ta'adda 3 da wasu mayaƙa 22 sun baƙunci lahira a Borno

An bude rumbunan da aka kulle a Kano
Gwamnatin Kano ta bude rumbunan kayan abinci da aka rufe a jihar Hoto: @Kyusufabba, @babarh
Asali: Twitter

Shugaban hukumar Muhyi Magaji, ya shaida wa jaridar The Punch a wata hira ta wayar tarho cewa masu rumbunan sun kawo kansu kuma an umarce su da su buɗe su sayar wa jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane alfanu aka samu kan kulle rumbunan?

Magaji ya ce a dalilin haka Kano ta fara ganin faɗuwar farashin kayan abinci.

A kalamansa:

“Matakin da hukumar ta ɗauka ya tilasta wa dillalan shigo da kayayyaki kasuwanni tare da rage farashin su.
"Mun ziyarci kasuwanni da dama da suka haɗa da kasuwar hatsi ta Dawanau, kasuwar Singer da kasuwar Kwari da dai sauransu.
"Idan ka je kasuwar Shuwari a Jigawa da Faskari da sauran kasuwannin jihohi makwabta, za ka ga farashin hatsi ya ragu idan aka kwatanta da baya."

A cewar Muhuyi, aikin ya yi tasiri sosai wajen rage tashin farashin hatsi da sauran kayayyakin masarufi a jihar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka bayin Allah da yawa a garuruwa 5 a jihar Arewa

Ya yi watsi da iƙirarin da shugabannin kasuwar hatsi ta Dawanau suka yi na cewa ba su tara kayan abinci da nufin haifar da ƙarancinsu ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rufe rumbunan ajiyan da hukumar ta yi, ya jawo muhawara sosai a faɗin jihar Kano.

Farashin Kayan Abinci Ya Fara Sauka

A wani labarin kuma, kun ji cewa farashin kayan abinci da ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar nan, ya fara sauka a wasu jihohi.

Farashin kayan abincin dai sun fara yin ƙasa a kasuwannin hatsi na jihohin Kano, Taraba da Neja bayan an fara gudanar da.zanga-zanga kan tsadar rayuwa ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel