Sabuwar Takaddama Yayin da Ake Zargin Mutuwar Dan Siyasa a Hannun Jami'an Tsaron CPG a Jihar Arewa

Sabuwar Takaddama Yayin da Ake Zargin Mutuwar Dan Siyasa a Hannun Jami'an Tsaron CPG a Jihar Arewa

  • Sabuwar hukumar tsaro ta CPG a jihar Zamfara ta fara gamo da cikas bayan zargin kisan wani dan siyasa a jihar
  • An yi ta cece-kuce bayan mutuwar wani dan siyasa mai suna Magaji Lauwali a hannun jami’an tsaron hukumar
  • Kwamnadan CPG, Kanal Rabiu Yandoto ya musanta hannu a kisan inda ya ce kafin fara aiki ma marigayin ya rasu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara – An yi ta cece-kuce bayan mutuwar wani dan siyasa a hannu jami’an tsaron Community Protection Guard (CPG) a jihar Zamfara.

Sai dai ana zargin dan siyasar mai suna Magaji Lauwali ya rasa ransa yayin artabu tsakanin CPG da kungiyar ‘yan sakai da aka dakatar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan bindiga a Arewa, sun kwato muggan makamai

Zargin kisan dan siyasa ta jefa hukumar CPG cikin wani hali a Zamfara
Sai dai kwamandan hukumar, Kanal Yandoto ya musanta zargin. Hoto: Community Protection Guard, Magaji Lauwali.
Asali: Facebook

Mene ake zargin hukumar a Zamfara?

Mutuwar dan siyasar ya jawo cece-kuce inda wasu ke zargin CPG da neman bata suna yayin da suke zargin Magaji da hannu a ayyukan ‘yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar tuni ta tsame kanta daga lamarin inda ta ce ta umarci bincike kan lamarin don gano gaskiya.

Har ila yau, Yahaya Galadima wanda aka cafke tare da marigayin ya ce an kai su ofishin CPG inda ake zarginsu da alaka da ‘yan ta’adda wanda suka musanta.

Galadima ya fadawa Daily Trust cewa bayan sun musanta zargin, jami’an sun daure su tare da kulle su a cikin daki kafin daga bisani a raba su, ya ce tun lokacin bai san meye ya faru da Magaji ba.

Ya ce:

“Sun yi mana dukan tsiya ba tare da ba mu abinci ba, idan ka duba hannaye na zaka ga ciwon daurin, daga bisani sun sake ni tare da ba ni hakurin abin da suka min.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

Martanin dan cikin marigayin

Nura Magaji Lauwali wanda dan cikin marigayin ne ya ce sun je ofishin don karbar wayar mahaifinsu inda suka kulle su tare da zargin ya yi barazanar kisan jami’ansu.

Ya ce sun tsare su tare da azabtar da su kan dole sai sun ba da shaidar karya kan mahaifin nasu inda suka kafa masa bindiga cewar sai ya fadi abin da suke so.

A cewarsa:

“Daya daga cikinsu ya nuna min bindiga inda ya ce sun hallaka baba na a cikin wani daki inda ya ce nima za su min haka idan naki bin umarninsu ba.
“Duk da haka naki amincewa amma kawu na ya bani shawar mu bi umarninsu don tsira da rayuwarmu inda suka tilasta ni ba da shaidar karya.”

Iyalan marigayin sun tabbatar da cewa kisan Magaji akwai siyasa tsantsarta a ciki babu tantama, cewar Premium Times.

Sai dai kwamnadan CPG, Kanal Rabiu Yandoto ya musanta hannu a kisan marigayin inda ya ce kafin ya fara aiki a hukumar marigayin ya rasu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Alia ya zargi neman rusa gwamnatinsa

Kun ji cewa, Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue ya zargi wasu da shirin kawo makiyaya jihar.

Alia ya ce akwai ‘yan jihar da ke hada baki don gayyatar makiyaya daga kasar Nijar don kawo cikas a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.