An Kama Shugaban APC da Wasu Mutane da Hannu a Kashe-Kashe a Ebonyi

An Kama Shugaban APC da Wasu Mutane da Hannu a Kashe-Kashe a Ebonyi

  • Jami'an tsaro sun kama mutane akalla 26 da ake zargi da ɗaukar nauyin tashin-tashinar da ta auku a garin Ekolo Edda a watan Disamba
  • Rundunar yan sandan Ebonyi tace daga cikin waɗanda suka shiga hannu har da shugaban APC na jiha da tsohon ciyaman
  • Lamarin dai ya faru ne ranar 26 ga watan Disamba, 2022, kuma mutane biyu suka mutu tare da ƙona gidaje

Ebonyi - Aƙalla mutane 26 suka shiga hannu kan kashe-kashe da ƙone-konen da aka yi kwanan nan a Ekolo Edda, ƙaramar hukumar Afikpo, jihar Ebonyi.

Punch ta rahoto cewa daga cikin wadanda aka cafke har da shugaban jam'iyyar APC na jiha, Stanley Okoro-Emegha, da tsohon shugaban karamar hukumar Afikpo ta kudu, Eni Chima.

Taswirar jihar Ebonyi.
An Kama Shugaban APC da Wasu Mutane da Hannu a Kashe-Kashe a Ebonyi Hoto: punchng
Asali: UGC

Rundunar yan sanda tace mutanen da ta cafke tana zarginsu da hannu a kashe-kashen da ƙone-konen da ya auku a yankin ranar 26 ga watan Disamba, 2022.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mai Hannu a Harin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja, An Gano Abu 3

Bayanai sun nuna cewa lokacin da rikicin ya ɓarke, mutum biyu ciki har da Insufektan 'yan sanda suka rasa rayukansu yayin da gidaje biyu suka ƙone ƙurmus.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ce ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abakaliki, babban birnin jihar ranar Litinin.

Tuhume-tuhumen da ake wa mutanen

Bayan kisan kai, Rundunar 'yan sandan tana zargin mutanen da kunna wuta, haɗin baki, fashi da makami da kuma mallakar bindigu da bisa ƙa'ida ba.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan, SP Chris Anyanwu, yace ana zargin mutanen da hannu a aikata ɗanyen aiki kuma ta sha alwashin gurfanar da su a gaban Kotu.

SP Anyanwu:

"Manyan wadanda ake zargi sun shiga hannu, haɗin kan da suka bayar wurin amsa laifukansu ya taimaka sosai wajen binciken gano gaskiya kan makasudin tashin-tashinar da ta auku."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta, Sun Yi Babbar Ɓarna a Jiha

A wani labarin kuma Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, Sun Tafka Barna

Rahotanni daga jihar Ribas sun tabbatar da cewa wasu yan baranda sun bude wa ayarin ɗan takarar gwamna wuta a jihar Rabas ranar Asabar da ta gabata.

Ɗan takaran wanda ya tsira daga harin, ya nuna danuwarsa kan yadda siyasar Ribas ke sauya akala zuwa ta zubda jini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel