Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Kashe Bayin Allah Bayan Gama Sallah a Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Kashe Bayin Allah Bayan Gama Sallah a Jihar Arewa

  • 'Yan bindiga sun kai kazamin hari kauyen Kwanar Dutse a jihar Zamfara saboda sun gaza biyan harajin N20m
  • Wani mazaunin garin ya ce 'yan ta'addan sun kashe mutum 10 jim kaɗan bayan kammala sallar la'asar ranar Laraba
  • Bayan kisan rayuka, maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna garin, har yanzun yan sanda ba su ce komai ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Tawagar ƴan bindiga karkashin jagorancin ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Damina, sun kashe mutum 10 a garin Kwanar Dutse da ke jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne sabida mazauna garin sun kasa biyan harajin N20m da suka ƙaƙaba musu a makonnin da suka shige.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya samu gagarumin goyon baya yayin da Kotun Koli ke dab da yanke hukunci

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.
Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 10 a Jihar Zamfara Saboda Sun Gaza Biyan Haraji Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Damina ya jagoranci daruruwan mayakansa zuwa cikin garin Kwanar Dutse 'yan mintoci ƙalilan bayan karfe 4:00 na yammacin ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanar Dutse da ke ƙarƙashin masarautar Dansadau a karamar hukumar Maru na daya daga cikin garuruwan da aka fi kai wa hare-hare a jihar Zamfara.

Yadda yan bindigan suka aikata ɗanyen aikin

Wani mazaunin Kwanar Dutse da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya shaida wa Premium Times ta wayar tarho cewa maharan sun afka musu ne bayan an idar da sallar la'asar.

Mutumin ya ce:

“Muna zaune a ƙofar wani masallaci lokacin da ‘yan ta’addan suka shigo cikin garin daga kowane lungu da sako suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
"Wasu daga cikin ƴan banga sun yi kokarin taka masu burki amma maharan sun fi su makamai. Nan take na ruga gidana, na jira abinda zai faru."

Kara karanta wannan

Miyagu sun harbe babban limamin Masallacin Jumu'a da ɗan acaɓa a Filato

'Yan ta'addan sun kona wasu shaguna da gidaje yayin harin, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Wani shugaban al’umma ya ce dan uwan sa na daya daga cikin wadanda ‘yan ta’addan suka kashe a harin da aka dauki tsawon sa’o’i ana yi, rahoton Blueprint.

Yan gudun hijira sun koma garin Ɗansadau

Wani mazaunin garin Dansadau wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya ce gidansa cike yake da ‘yan gudun hijira daga Kwanar Dutse.

"Su kan dora wa al’umma makudan kudaden haraji da suka kai na miliyoyin naira, idan kuma suka kasa biya sai su je su kashe su kamar dabbobi,” inji shi.

An tattaro cewa bayan kisan mutum 10, yan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna garin da dama.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, bai amsa kira da sakonnin da aka aika masa kan harin ba.

Kara karanta wannan

Bayin Allah sama da 100 sun mutu yayin da bama-bamai suka tashi a wurin taro kusa da Masallaci

Sojoji sun samu nasara a Katsina da Zamfara

A wani rahoton kuma Dakarun sojoji sun samu nasarar halaka hatsabiban yan bindiga tare da ceto mutame daga hannunsu a Zamfara da Katsina.

Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Ibrahim Yahaya, ya ce sojojin sun halaka yan bindiga 10, sun kwato muggan makamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel