An Karrama Wasu Jami’an ’Yan Sanda 4 a Kan Wata Babbar Bajinta da Suka Yi a Jihar Arewa
- Rundunar 'yan sanda ta karrama wasu jami'an ta huda hudu da suka ƙi karbar cin hancin naira miliyan 8.5 daga hannun dan bindiga
- Kwamishinan 'yan sanda na jihar Taraba, David Iloyalonomo ya karrama jami'an da ke aiki a jihar tare da tura sunayen su ga Sufeta Janar
- Legit Hausa ta ruwaito maku cewa wani dan bindiga ya ba jami'an 'yan sandan cin hanci a lokacin da suka tare shi don gudanar da bincike
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Taraba - Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta karrama jami’an ta guda hudu bisa kin karbar cin hancin naira miliyan 8.5 daga hannun wani dan bindiga a yayin da suke gudanar da bincike.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar David Iloyalonomo, ya baiwa jami’an ‘yan sandan hudu kyauta a ofishinsa dake hedikwatar ‘yan sandan jihar Taraba.
Lokacin da wakilin Channels TV ya ziyarci shingen binciken, ya zanta da Ngamarju Gambo, daya daga cikin jami’an da suka kama dan bindigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a kai sunayen jami'an gaban Sufeto Janar don karramawa
Gambo ya bayyana cewa matakin da suka dauka na yaki da cin hanci da rashawa da kuma neman zaman lafiya a fadin kasar nan ne ya sa su ka ki karbar cin hancin.
A cewarsa, a ranar sun shaida wa wanda ake zargin cewa ba ya cikin tsarinsu na yin wani abu da zai iya bata sunan rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Iloyalonomo ya bada tabbacin cewa zai kai sunayen jami’an hudu ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, domin samun karin girma da kuma karramawa.
Dan bindigar na bada hadin kai wajen bincike - Iloyalonomo
Ya kuma bayyana sunayen jami’an ‘yan sandan guda hudu da suka hada da Sufeto Difference Tih AP/NO 362424, Sufeto Ngamarju Gambo AP/NO 362385, Sufeto Usman Haruna AP/NO 246517 da Kofur Zarudeen Mamuda F/NO 517199.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin yana ba ‘yan sanda hadin kai a ci gaba da gudanar da bincike kan ayyukan garkuwa da mutane da suka yi a baya.
Ya bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin tare da wasu a gaban kotu bisa laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran su.
Taraba: Yan sanda sun ki karbar cin hancin naira miliyan 8.5
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Taraba sun tare wata motar dan bindiga da ake zargin mai garkuwa da mutane ne.
A yayin da suka yi yunkurin binciken motar da tuhumarsa, wanda ake zargin ya ba jami'an cin hancin naira miliyan 8.5 da ake zargin kudin fansa ne da ya karba a ranar.
Sai dai jami'an sun ki amincewa da wannan cin hanci inda suka kai shi zuwa ofishin su, tare da tuhumar sa, kuma ya amsa laifin yin garkuwa da mutane.
Asali: Legit.ng