Yadda Mai Garkuwa da Mutane Ya Ba Jami’an Mu Cin Hancin Naira Miliyan 8.5 – ’Yan Sanda

Yadda Mai Garkuwa da Mutane Ya Ba Jami’an Mu Cin Hancin Naira Miliyan 8.5 – ’Yan Sanda

  • Wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne ya ba jami'an 'yan sanda cin hancin naira miliyan 8.5 bayan da suka kama shi a Jalingo, jihar Taraba
  • Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an sun tare motar da mai garkuwan ke ciki a ranar Litinin, inda ya nemi ba su cin hanci don su kyale shi ya tafi
  • Sai dai kwamishinan'yan sandan jihar, Joseph Eribo ya ce jami'an ba su karbi kudin ba, kuma sun kama wanda ake zargin domin gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Taraba - Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba a ranar Talatar da ta gabata ta ce jami’anta sun ki karbar cin hancin naira miliyan 8.5 da aka ba su bayan sun tare wata mota a Jalingo.

Kara karanta wannan

Yadda ma'aikacin banki ya yi karyar 'yan bindiga sun sace shi saboda bashin naira miliyan 1.7

Joseph Eribo, kwamishinan ‘yan sandan jihar ne ya bayyana haka a lokacin da yake holen wasu masu laifi a hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Jalingo.

Taraba: Dan bindiga ya ba jami'an 'yan sanda cin hancin N8.5m
Taraba: Abin da ya faru bayan wani ɗan bindiga ya ba jami'an 'yan sanda cin hancin N8.5m. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A cewar shugaban ‘yan sandan, lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 9:45 na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun ki karbar cin hanci

Ya ce jami’an sashen PMF, bataliya ta 40 da ke bakin aiki a Yaggai, da ke kan hanyar Jalingo-Yola, sun tare wata mota kirar Toyota Starlet mai lamba YLA 321 ZY a daren.

Mista Eribo ya ce an samu naira miliyan 8.5 da ake zargin kudin fansa ne a hannun wanda aka kama mai suna Aliyu Mohammed, dan asalin garin Mubi ta jihar Adamawa.

"Wanda ake zargin ya bai wa jami'an PMF cin hanci, inda ya bukaci su karbi duka kudin don su kyale shi ya tafi, amma jami'an suka ki yarda kuma suka kama shi,"

Kara karanta wannan

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fi ko ina yawan masu garkuwa da mutane, in ji Seun Kuti

In ji Mista Eribo, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

An kama masu garkuwa da mutane a Taraba

Ko a jihar Kaduna, The Cable ta ruwaito yadda wani mai garkuwa da mutane ya ba jami'in dan sanda cin hancin naira miliyan daya lokacin da aka kama shi a wani otal.

A hannu daya, jami’an hukumar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Taraba.

An kama su ne a garuruwan Jalingo, Lau da Yorro, ciki har da wanda ake zargin su ne suka shirya yadda aka yi garkuwa da wani basarake mai daraja ta uku na Pupule da dai sauransu.

Matashi ya dauki ransa saboda tsohuwar matarsa ta yi aure

A wani labarin kuwa, wani matashi da ke gadi a wata makarantar kwaleji da ke jihar Kano ya rataye kansa har lahira saboda tsohuwar matarsa ta yi wani sabon aure.

Rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da lamarin, inda ta ce matashin mai suna Nuruddeen Shehu ya rataye kansa a cikin wani aji da ke a makarantar da ya ke gadin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel