Gobara ta kone shaguna 70, ta babbake tsuntsaye fiye da dubu 8 a Yola

Gobara ta kone shaguna 70, ta babbake tsuntsaye fiye da dubu 8 a Yola

- Akalla tsuntsaye 8,845 ne suka babbake a wata gobarar tsakar dare da ya afku a babban kasuwar Jimeta da ke Yola, babbar birnin jihar Adamawa

- Alhaji Idris Sa’idu, Shugaban kungiyar dilallan kaji reshen jihar Adamawa ya bayyana hakan

- Sa'idu ya alakanta gobarar ga matsalar wutar lantarki

Kimanin tsuntsaye 8,845 ne suka babbake a wata gobarar tsakar dare da ya afku a babban kasuwar Jimeta da ke Yola, babbar birnin jihar Adamawa, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Alhaji Idris Sa’idu, Shugaban kungiyar dilallan kaji reshen jihar Adamawa ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Talata, 19 ga wat Maris.

Sa’idu ya bayyana lamarin wanda ya afku a tsakar daren ranar Litinin da misalin karfe biyun dare ya kuma lalata shaguna da dama.

Gobara ta kone shaguna 70, ta babbake tsuntsaye fiye da dubu 8 a Yola
Gobara ta kone shaguna 70, ta babbake tsuntsaye fiye da dubu 8 a Yola
Asali: Twitter

Ya alakanta gobarar ga matsalar wutar lantarki.

Dr Muhammed Suleiman, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Adamawa, yayinda yake tabbatar da faruwar lamarin ya kara da cewa ba a rasa rai ko daya ba.

KU KARANTA KUMA: Kano: Na riga na kafa majalisar Abba gida-gida - Kwankwaso

Suleiman yace hukumar ta duba yawan barnar da ya afku domin yiwuwar sanya baki a lamarin.

Mu’ azu Yola, Shugaban sashin tsuntsaye na ma’aiktar Adamawa ma ya tabbatar da lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel