Bambanci da Amfanin Tsarin Shugaban kasa da Firayim MInista da Ake So a Koma a 2031
- A salon mulkin duniya, tsarin damukaradiyya shi ne ya fi karbuwa duk da akwai wasu tsare-tsaren dabam
- Akwai kasashen da ake mulkin sarauta kamar yankin Larabawa, akwai masu fama da kama-karyar sojoji
- Rahoton nan ya yi bayanin yadda tsarin Shugaban kasa da na Firayim Minista yake aiki a kasashen Duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A salon damukaradiyya akwai nau’in mulki na shugaban kasa kamar yadda ake gani a Najeriya, akwai tsarina Firayim Minista.
Kafin salon da ake kai a yau, an jarraba salon mulki na Firayim Minista kafin sojoji su kashe Abubakar Tafawa-Balewa a Junairun 1966.
Salon mulkin shugaban kasa
1. Mai girma Shugaban kasa yake da cikakken iko a tsarin mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Shugaban kasa zai ruguza matakin da majalisa ta dauka. A Najeriya shugaban kasa zai iya watsi da kudirin ‘yan majalisa.
3. Shugaban kasa yana da tsayayyen wa’adi, ba za a iya sauke shi ba saboda rashin na’am a majalisa sai a inda doka ta bada dama.
4. Shugaban kasa yana da ikon yin afuwa ga wadanda aka samu da laifi. Hakan ta faru da Jolly Nyame da Joshua Dariye a 2022.
5. Mafi rinjayen al’ummar gari suka zabi shugaban kasa ba kuri’ar majalisa ta kai shi ba.
Salon mulkin Firayim Minista
1. A nan, akwai alaka mai kyau tsakanin ‘yan majalisa da shugaban da yake kan mulki. ‘Yan majalisa duk abokan aikin Firayim Ministan kasa ne.
2. Akwai nau’i biyu na shugabanni – shugaban kasa ko basarake (kamar Nnamdi Arzikwe ko Sarauniya Elizabeth) da Firayim Minista mai cikakken iko.
3. Firayim Minista zai cigaba da mulki muddin jam’iyyarsa ta na da rinjaye a majalisa kuma ’yan majalisar sun gamsu da irin rawar da yake takawa.
Amfanin tsarin shugaban kasa
1. Kowa da aikinsa
Doka ta tsarawa shugabanni, ‘yan majalisa da alkalai aikinsu, babu wanda zai yi katsalandan, kuma ana iya takawa mai mulki burki.
2. Aiki da kwararru
A tsarin nan shugaban kasa zai fi samun damar nada kwararru domin yana da zabin yin aiki da wanda ya dace, ba a tsuke shi da majalisa ba.
3. Tsayayyen lokaci
Rahoton ByJus ya ce a irin wannan tsari, ba a yawan shakkar rugujewar gwamnati domin mai mulki bai faya sauka ba har sai wa’adinsa ya cika.
4. Rage hayaniyar siyasa
A wannan salo, rikicin siyasa bai cika tasiri sosai a gwamnati ba. Shugaban kasa yana da ikon jawo har ‘yan wasu jam’iyya a cikin gwamnatinsa.
Amfanin tsarin Firayim Minista
1. Hadin-kai tsakanin Firayim minista da ‘yan majalisa
2. Hana kama karya a mulki
3. Takawa gwamnati burki
Matsalar tsarin shugaban kasa
1. Kama-karyar masu mulki
Tun da majalisa ba ta da iko sosai wajen hana shugaban kasa sakat, wannan ya kan kawo shugaban da ke mulki ya rika yin kama-karya.
2. Sabanin fada da majalisa
Rahoton ya ce a kan sabu ta-ta-bur-za tsakanin ‘yan majalisa da fadar shugaban kasa. An ga yadda rrin wannan sabani ya kan kawo cikas.
3. Taurin kai
A karshe a kan zargi shugabannin kasashen da ke mulki a irin wannan tsari da taurin-kai.
Matsalar tsarin Firayim Minista
1. Babu rabon aiki:
Babu damar da kowa zai samu hurumin aiki musamman daga ‘yan adawa a majalisa.
2. Rashin cancanta:
Za a iya zaben mutum daga mazaba kuma ya dare kan kujerar minista mai muhimmanci a tare da la’akari da kwarewarsa a kan aikin ba.
3. Rashin tabbas
A nan kuwa, za a iya yin waje da Firayim Minista yana tsakiyar wa’adinsa a maimakon a jira lokacin da za a gudanar zabe a fadin kasa.
4. Toshe kofa
Wannan tsari yana hana mulki ya shiga hannun jam’iyyun adawa, a dalilin haka ana rasa kwararrun da suka cancanta su taya gwamnati aiki.
5. Aiki a asirce
Cikin abin da yake jawo ana kushe tsarin akwai yadda ake gudanar da gwamnati a asirce, talakawa ba su da masaniyar abubuwan da ke wakana.
Su wanene kasashe ake da shugaban kasa?
Kasashen suna da yawa, amma daga ciki akwai:
1. Najeriya
2. Sin
3. Cili
4. Indonesiya
5. Honduras
6. Laberiya
7. Malawi
8. Nijar
9. Falau
10. Fanama
11. Amurka
12. Zambiya
13. Zimbabwe
14. Uruaguay
15. Turkiyya
Su wane Kasashe ake da Firayimin Minista?
1. Birtaniya
2. Ajentina
3. Balarus
4. Burundi
5. Kamaru
6. E/Gini
7. Jibuti
8. I/Kwas
9. Feru
10. Sanagal
11. Koriya ta Kudu
12. Siriya
13. Ruwanda
14. Togo
15. Tunisiya
Canza dokar kasa a Najeriya
Ana da labari Sanata Godswill Akpabio ya sanar da ‘yan kwamitin mutum 45 da za su gyara tsarin mulkin Najeriya a majalisar dattawa.
Za a hada da 'yan majalisar jihohi wajen yin garambawul a kundin tsarin mulkin Najeriya. Sanata Barau Jibrin ne zai jagoranci wannan aiki.
Asali: Legit.ng