Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Hukumar Kayayyakin Masarufi Don Daidaita Farashin Kayan Abinci
- Gwamnatin tarayya ta ce za ta kafa wata hukuma da za ta rinka saka ido kan hawa da saukar farashin kayan masarufi a Najeriya
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce hukumar za ta daidaita farashin kayan abinci
- Haka zalika Shettima ya lissafa wasu hanyoyi da gwamnatin tarayya ta ke bi don ganin abinci ta wadata a kasar tare da samuwa cikin sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin kafa hukumar kayayyakin masarufi da za ta daidaita tashin farashin kayayyakin abinci a kasar.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen wani taro kan sauyin yanayi, tsarin abinci da aka gudanar a Abuja.
Bayanin nasa na zuwa ne bayan wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta umurci gwamnatin tarayya a ranar 7 ga Fabrairu, 2024, da ta daidaita farashin kayayyaki da na man fetur cikin kwanaki bakwai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudurin gwamnatin Tinubu kan samar da abinci
A cewar Shettima, za a bai wa hukumar aikin tantancewa da daidaita farashin kayan abinci, da kuma kula da tsarin tanadin abinci na kasar baki daya, rahoton The Cable.
Ya ce samar da abinci na daya daga cikin fannoni takwas da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a matsayin masu muhimmanci a shirin sa na 'sabuwar Najeriya'.
Mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin Tinubu ta ba da himma wajen ganin ta dawo da martabar kasar noma a fadin Najeriya.
Gwamnati za ta bunkasa harkar noma - Shettima
A cewarsa, akwai shirye-shiryen dawo da martabar kadada miliyan 10 na gurbatacciyar kasa a cikin iyakokin kasar a matsayin gudunmawar da ta bayar ga shirin AFR100.
Shettima ya kuma sanar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Tinubu da kamfanonin injuna domin kara samar da filayen noma, da bunkasa harkar noman baki daya.
Ya kuma bayyana yadda ake ci gaba da tallafa wa harkar noma ta hanyar samar da kudade daga babban bankin Najeriya (CBN).
Gwamnatin tarayya za ta fitar da ton 42,000 na kayan abinci
A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta ce za ta fitar da ton 42,000 na kayan abinci don karya farashin kayan abincin a kasuwanni.
Hakan na zuwa ne bayan da farashin kayan abinci suka yi tashin gwauron zabi, wanda ya kara jefa 'yan Najeriya a cikin mawuyacin hali.
Ministan watsa labarai, Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a Abuja, inda ya ce kayan abincin sun hada da shinkafa, gero da garin kwaki.
Asali: Legit.ng