Inganta noma: FG ta fitar da N600bn don tallafawa manoma

Inganta noma: FG ta fitar da N600bn don tallafawa manoma

- Gwamnatin Najeriya ta ware wasu makudan kudade har naira biliyan 600 don tallafawa manoma da ke fadin kasar

- Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono ya sanar da hakan a yayin kaddamar da shirin manoma a jihar Kano

- Za a mika kudin ga mutum 2.4 miliyan daga cikin manoman fadin kasar nan don daukar dawainiyar ayyukansu

Gwamnatin tarayya ta ware wasu makudan kudade har naira biliyan 600 don tallafawa manoma da ke fadin kasar nan.

Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono ya sanar da hakan a yayin kaddamar da shirin manoma a jihar Kano.

Karin tabbacin hakan shine wallafar da hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi a shafin Twitter.

Ya ce an yi nufin mika kudin ga mutum 2.4 miliyan daga cikin manoman fadin kasar nan don daukar dawainiyar ayyukansu.

Inganta noma: FG ta fitar da N600bn don tallafawa manoma
Inganta noma: FG ta fitar da N600bn don tallafawa manoma Hoto: Reuters
Asali: UGC

"Gwamnatin tarayya ta fitar da N600 biliyan don inganta noma a fadin kasar nan. Ministan aikin noma da raya karkara, Sabo Nanono ya ce manoma 2.4 a fadin kasar nan ne za su amfana," Bashir Ahmad ya wallafa.

KU KARANTA KUMA: Jihohi masu talauci: Tambuwal ya yi watsi da rahoton NBS

A gefe guda, mun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shawo kan matsalar tsaro da ya addabi yankin arewa ta yadda noma zai dawo.

A wata takarda da Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce idan har ba a shawo kan matsalar tsaro ba, ta yuwu hakan ya zama babbar matsala ga kasar baki daya.

Kamar yadda yace, "Noma ba wai aiki kadai bane ga mafi yawan jama'ar kasar nan, illa ya kuma kasance sana'a ce da ke jinin dukkan 'yan arewa.

"Noma da arewa abu daya ne. Amma rashin tsaron da yankin ke fama da shi yana kawo cikas ga harkar noma.

"A don haka nake kira ga gwamnatin tarayya da ta hada kai da jihohin da ke yankin don shawo kan matsalar tsaro. Rashin shawo kan matsalar tsaro zai iya zama matsalar da dukkan kasar nan za ta koka a kai."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel