Jigon PDP Kuma Tsohon Kakakinta Zai Kwana a Gidan Kaso Bayan Gwamnatin APC Ta Zargeshi da Laifi 1
- Kotun Majistare a birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi ta tsare jigon PDP a gidan kaso kan zargin bata suna da karya
- Ana zargin Chika Nwoba da aikata laifuka guda uku da suka hada da barazanar kisa da bata suna da kuma ba da bayanan karya
- An gurfanar da Chika ne wanda shi ne tsohon kakakin jam’iyyar a jihar a yau Talata 13 ga watan Faburairu kan zarge-zargen
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi – Jigon jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Ebonyi ya shiga matsala bayan tsare shi da aka yi a gidan kaso.
Ana zargin Chika Nwoba da aikata laifuka guda uku da suka hada da barazanar kisa da bata suna da kuma ba da bayanan karya.
Mene ake zargin jigon PDP?
Kotun Magistare da ke birnin Abakaliki a jihar ita ta umarci tsare Chika a gidan gyaran hali bayan gurfanar da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gurfanar da Chika ne wanda shi ne tsohon kakakin jam’iyyar a jihar a yau Talata 13 ga watan Faburairu kan zarge-zargen.
Premium Times ta tabbata da cewa an kama Chika ne tun a ranar Lahadi 11 ga watan Faburairu bayan korafin da aka shigar.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu a jihar, Oguzor Offia-Nwali shi ya gabatar da korafi kan Chika a ofishin ‘yan sanda.
Nwali ya zargi Chika da wallafa wasu bayanai a shafin Facebook inda ya ke bata masa suna da cewa ya karkatar da wasu kudaden jihar.
Martanin lauyoyin a shari'ar
Lauyan wanda ake zargi, C N Ufufu ya nemi kotun ta ba da belin wanda ya ke karewa bayan karanto laifukan.
Lauyan ya ce laifin da ya aikata ya cancanci beli inda ya ce masu karar ba su samu amincewa daga kwamishinan shari’a a jihar ba.
Mai Shari’a, Lilian Ogodo ta umarci tsare shi a gidan kaso inda ta ce inda ya dace a gudanar da shari’ar ita ce babbar kotun jihar, cewar Daily Post.
An cafke mata da kisan kai a Legas
Kun ji cewa, rundunar ‘yan sanda ta cafke wata mata da zargin kisan makwabciyarta a Legas.
Matar mai suna Cynthia ta yi ajalin makwabciyarta ce mai suna Barakat kan wata ‘yar hatsaniya.
Asali: Legit.ng